Dole ne a kalli Bidiyo Yadda Aka Kama Ɓarawon da Ya saci Sadaki ana Tsaka da Ɗaurin Aure a Masallaci. Lallai Wannan Babbane
Wata Sabuwa An Kama Ɓarawon da Ya saci Sadaki ana Tsaka da Ɗaurin Aure a Masallaci
A yau Juma’a bayan idar da Sallah a masallacin Juma’a na Al-Noor dake titin IBB Wuse 2 Abuja aka kama wannnan Barawo da ya sace kudin Sadaki a dai-dai lokacin da ake daura Auren wata budurwa da Saurayinta.
Rahotanni dai solar bayyana cewa, sadakin ya kai Naira Dubu Dari.
Sai dai an karbi sadakin daga hannun barawon inda ya sha duka a hannun masu tsaron masallacin.
Haka kuma ya yi nadama bisa ga abinda ya aikata.
Wannan shi ne karo na biyu da aka taba sace kudin sadaki a wannan masallacin.
An dai sace kudin kafin a biya sadakin wanda ya yi sanadiyar daura auren bashi sai daga baya angon ya sake samsun kudin ya biya sadaki.
Ga bidiyon abinda ya faru nan munkawo maku asha kallo lafiya.