Dole Matan Arewa Su Guji Zaman Jangwam, Inji Hajiya Fatimma Lamaj

- Advertisement -

Dole Matan Arewa Su Guji Zaman Jangwam, Inji Hajiya Fatimma Lamaj

Daga Nasiru Adamu

A wata tattaunawa da wakilinmu ya yi da shugabar kungiyar masu kula da Sana`o´i a jihar Kaduna ´´MOPPAN“, kuma shugaba a kungiyar LAMAJ Movie, sanan kuma mataimakiyar shugaba a kungiyar Kaniwood ta kasa.

Tattaunawar ta kumshi yanayin da matan Arewa ke ciki, na rashin ko in kula da neman ilimi ko sanaar dogaro da kai, sai abinda miji ya kawo da shi ake dogara, akan haka ne ta yi wa wakillin namu karin haske na yadda ya kamata mace ta kasance a gidan mijinta. Ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance
Assalammu alaikum Hajiya masu karatun mu za su so jin sunanki da kuma matsayinki a kungiyar nan ta ´´MOPPAN“
Wa alaikumussalam sunana Hajiya Fatima Ahmad Ibrahim wadda aka fi sani da Hajiya Fatima Lamaj, kuma shugaba a kungiyar MOPPAN a nan jihar Kaduna, kuma ni shugabace a kungiyar LAMAJ ta kasa, saanan ina rike da mataimakiyar shugaban kungiyar mata ta shirya finafinan KANNYWOOD
Hajiya ita wannan kungiyar taku ta MOPPAN, wanne irin aikace aikace kuke yi a cikinta?
Ita wannan gungiyar tana da wani reshe a karkashinta da ake kira ´Arewa Fim Mekas, wandda ita kuma ta kumshi rassa kusan guda bakwai a karkashinta kamar ´Gilt of producers, Administrators, Editors, da sauransu.

Kuma babban aikin wanna kungiya shine tace finafinai kafin a sakesu zuwa kazuwanni, don jama` su kalla. Duk da ko ba shine kadai aikin waannan kungiyar ba.

Hajiya a matsayinki na mace yar Arewa, kuma mai fafutukan neman na kanta, wanne kira za ki yi ga yanuwanki matan Arewa wajen zaburantarwa don neman na kai ta hanyar sanaa ko aiki, don tallafawa iyalin ta?
To na farko dai abin da zance shine ni kaina matar aurence, wannan bai hana ni neman na kainaba kuma sau da yawa ni ke taimokon mijina wajen daukar dawainiyar gidasa ta fannin abinci da kudin makarantar yayanmu, kma abu na biyu shine ina ganin lokaci ya wuce na zaman jangwam ga mata, domin bai kamata ki jiran komai sai an kawo maki, sabo da dawainiyar da namiji ke da shi akan iyalin ya yi yawa ya kamata kowace mace ta tausayawa mijinta, ta hanyar zage damtse dommin yin wata sanaa koya take, saboda akwai kananan sanao´i da bassa bukatar babban jari.

Domin yau idan abin Allah ya kiyaye ace baki tare da mijinki, sakamakon mutuwa ko rabuwa, me kike tsammanin zai faru? musamman idanakwai yara a tsakaninku
Sannan abu na biyu da nake jawo hankalin matan Arewa shine neman ilimi, domin da shine duk wani mutum ke cin ribar zaman duniya da lahira, kuma matukar mace daya ta zamto mai ilimi daidai take da al`umma, kamar yadda Manzon Allah (saww) ya fada, a ciki hadisin sa.

Hajiya mafi yawan alumar Arewa na kallon sanaar fim sai ‘yan iska ke yinta, a matsayinki na shugaba a fanin duba tsarin ingancin fimafimai me zaki ce akan haka?
Shi Abin da mutumin Arewa ke mantawa da shi, shine bai cika kallon alfanun abu ba saidai ya kalli aibin sa, da ace ya fi kallon amfanin da sakonin da finafinai ke badawa, da zai fahimci wa´azi ne yawancin finafinai ke yi a zahiri da suka shafi dukkanin janibobin rayuwar mutane ake misaltawa.

Sauda yawan mutane sukan ga wani mumunan yanayi wani ya fada a fim sakamakon wani aiki da ya yi, kuma shi mai kallo ya san cewa shima yana aiki irin wannan, cikin hukuncin Allah sai ka ga ya bari, kamar yadda karin maganannan ke cewa ´´Gani ga wane ya ishi wani tsoran Allah“

Kuma shi iskanci janibinsa daban, domin mafi yawan mutane kowa da irin nasa iskancin da yake yi, saidai na wani yafi na wani ,hasalima akwai dayawan fitatun yan fim da muke da su mahaddata alkur´ani ne.

A lokaci guda kuma ba wai ina musanta cewan babu yan iskan da ake fada bane. amma dai kar ai masu kudin goro ko kuma a bata sana`ar fim.

Hajiya daga karshe wane kira zaki yi ga al´umma, da kuma su kansu masu shirya finafinan hausa?
To babban kiran da nake da shi shine kowane ban gare su ji tsoron Allah, Su masu shirya finafinai su san cewar duk wani abu da dan fim zaiyi duniya zata ganshi kuma masu bakin alatsine sunan ba kyalewa za su yi ba, kuma duk wanda ya koyar da wata bidala har wani
ya yi koyi da ita, yana da kamashon ta a gun Allah.

To Hajiya mun gode
To nima na gode

- Advertisement -