Dokar Ta-Baci Ba Zai Magance Matsalar Tsaro Ba — Gwamna Masari

0
96

Dokar Ta-Baci Ba Zai Magance Matsalar Tsaro Ba — Gwamna Masari

Sojojin Solar Kara Jaddada Aniyar  Fatattakar ‘Yan Boko Haram

Daga Bello Hamza Da Maigari Abdulrahman,

Gwamnan jihar Kastina, Aminu Bello Masari, ya ce, saka dokar ta-baci da wasu ke kira a saka ba zai magance matsalar tsaron da ya ke damun Najeriya ba.

Gwamnan ya fadi hakan ne yayin da ya ke amsa tambayoyin ‘yan jarida jim kadan bayan ganawa da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari a fadar shugaban kasa da ke Abuja, ranar Alhamis.

A ranar Talata ne dai majalisar wakilai ta yi kira ga shugaban kasa Buhari, da ya saka dokar ta-baci a Najeriya domin shawo kan matsalar tsaron da ke addabar Najeriya.

To sai dai, a cewar Gwamnan, babu wadatattun sojojin da za a yi anfani da su wurin tabbatar da dokar idan ma an saka, duba ga cewa tuni aikin samar da tsaro ya ci gaban sojojin a fadin kasar.

Haka ma, gwamnan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su guji siyasantar da matsalar tsaron da ke addabar kasar, a maimakon haka, neman kawo gyara ne ya fi dacewa a wannan halin da kasar ke ciki.

Da yake magana kan batun rashin yiyuwar iya yinm kasafin kudin Mayu ga jihohi, gwamanan ya yi kira ga gwamnati da ta bi hanyoyin da ya dace don ganin hakan ba ta faru ba. Rashin biyan kudin ga jihohi, zai iya kara tabarbarar da aikin samar da tsaro, a cewar sa.

Shugaban rundunar sojojin Nijeriya, Lt.- Gen. Ibrahim Attahiru, ya jaddada aniyar rundunar na tabbatar da fattatakar ‘yan kungiyar ta’adda na Boko Haram daga cikin Nijeriya gaba daya.

Attahiru ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da manema labarai a garin Maiduguri ranar Alhamis.

Ya ce an sha samun  nasarar a kan ‘yan Boko Haram sau da yawa, za kuma a cigaba da samun nasara a kan su har sai an kakkabe su daga Nijeriya gaba daya.

“Zamu fuskanci ‘yan Boko Haram, mun kuma kuduri aniyar tabbatar da mun yi nasara a kan su tare da kora su daga Nijeriya gaba daya, ” inji shi.

Shugaban rundunar yana ziyartar hedikwatar rundunar ‘Operation Lafiya Dole’ da ke Maiduguri ne a karo na biyar tun da aka nada shi a matsayin shugaban rundunar sojojin Nijeriya, ya ce ziyara a kai akai yana kara karfafa sojojin yana kuma samar da daman sauraron matsalolin da suke fuskanta don a yi maganin su.

Ya kuma kara da cewa, ya kawo ziyarar ne don ya mika sakon fatan alhairi daga shugaban kasa Muhammadu Buhari a kan kokarin da suke yi a fagen fama.

Ya kuma sanar da dakarun cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana shirye na basu dukkan goyon bayan da suke bukata don su samu nasara a yaki da ta’addanci da suke yi a yankin Maiduguri da ma fadin Nijeriya gaba daya.

Tunda farko a jawabin maraba, shugaban rundunar ‘Operation Lafiya Dole’, Maj.–Gen. Farouk Yahaya, ya yaba da ziyarar da shugaban rundunar sojin ya ke kawowa akai akai, ya ce, hakan yana karfafa zukatan sojojin a fage fama.

Shugaban sojojin ya kuma ziyarci asibitin sojoji na 7 Division Maiduguri inda ya gana da wadanda suka ji raunuka a fagen fama.

What's On Your Mind?