Direba Da Karen Mota Sun Yi Wa Mai Cutar HIV Fyade

0
223

Direba Da Karen Mota Sun Yi Wa Mai Cutar HIV Fyade

Wani direba da karen motarsa solar yi wa wata matashiya mai shekaru 25 fyade a kasar Afirka ta Kudu.
Sun yi wa matashiyar mai dauke da cutar sida fyade kafin su jefar da ita a gefen hanya a yankin KwaZulu-Natal da ke Kudu maso Gabashin kasar.

Matashiyar mai suna Belram, ta bayyana wa jami’an tsaron Rusa cewa, ta ji tsoron sanar da wanda suka yi mata fyaden tana dauke da cuta mai karya garkuwar jiki.

Ta ce “tsoron rasa rai na ne ya hana ni bayyana musu cewar ina dauke da cutar.”

Kalli Bidiyon Yadda Ummi Rahab ta bayyana yadda taji a lokacin da aka yi mata fyade

Beltram ta ce ta shiga motar ne don kai wa

saurayinta ziyara, kamar yadda ta saba.

Kazalika, ta ce bayan daukar lokaci suna tafiya, ta tambayi karen motar dalilin rashin mutane a motar.

Wanda daga wannan lokaci ne ya sanya wani kyalle ya rufe mata baki, sannan suka keta mata haddi.

Sai dai, Kakakin ’yan sandan KwaDukuza, Nqobile Gwala, ya tabbatar da faruwar lamarin bayan an shigar musu da korafi a zargin a caji ofis na Verulam.

Daga @aminiya.dailytrust.com

What's On Your Mind?