Dimbin Falalar Ciyar Da Mai Azumi

0
158

Dimbin Falalar Ciyar Da Mai Azumi

A uzu billahi minas shaidanir rajim. Bismillahir rahmanir rahim. Wa sallallahu alan Nabiyyil karim. Assalamu alaikum warahmtullahi Ta’ala wa barkatuh. Masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan makon domin cigaba da darasinmu kan abin da ya shafi Azumin Ramadan.

A takaice, yin sadaka da kyauta abubuwa ne ma su dimbin lada ko da ba da azumi ba, ballantana kuma lokacin azumin da ake ninninka wa Bayi ladan ibadunsu. A yi kokarin ciyar da masu azumi, saboda duk wanda ya baiwa mai azumi abincin buda baki; Allah zai ba shi ladan azumi baki daya baya ga nashi da ya yi. Misali, idan mutum ya ciyar da masu azumi 100, Allah zai ba shi ladan azumi 100 baya ga nashi da ya yi.

Manzon Allah (SAW) ya fi kowa kyauta kuma yana yi a ko wane lokaci, amma kamar yadda Hadisin Abdullahi bin Abbas ya nuna a ruwayar Bukhari, babu lokacin da ya fi yi kamar a watan Ramadan. Don haka, mu yo kokarin koyi da shi (SAW).

Hukunci Yin Aswaki Da Azumi Da dandana Wani Abu

Hadisi ya zo daga Amiru dan Rabi’ata cewa sau da dama ya ga Manzon Allah (SAW) yana yin aswaki da azumi a bakinsa. Wannan yana nuna mana ya halasta a yi aswaki da azumi kenan.

Hukuncin wanda maziyyi ko maniyyi ya fito masa alhali ya na azumi daga bakin Aminu Daurawa

Uwar Muminai Aisha (RA) da Malam Ada’u bin Rabaha solar saukaka a kan cewa idan bakin mutum yana wari zai iya amfani da wani abin da zai hana bakin wari amma kar ya kai ga makwogoro. Bisa dogaro da wannan, malamai solar ce idan mutum zai iya amfani da makilin ba tare da ya karya masa azumi ba (ya shiga makwogoro zuwa ciki); babu laifi ya yi hakan. Amma wanda ya san ba zai iya ba to kar ya yi.

Haka nan mace idan tana girki za ta iya dandana gishiri amma ta tofar kar ta bari ya shiga cikinta. An yi saukin ne domin idan wata ta yiwa maigida girki gishiri ya yi yawa; wani abu mara dadi zai iya faruwa, shi ya sa ita ma aka saukaka mata ta dandana don samun maslaha.

Abubuwan Da Ba Su Karya Azumi

Akwai abubuwan da Musulunci ya yi sauki a kai na zamani wadda idan an aikata su; ba sa karya azumi.

Idan rana ta yi zafi sosai sai ya kasance mutum ya shiga dan kududdufin ninkaya (swimming pool) ya yi wanka azuminsa bai karye ba. Malamai solar ce an yi rangwamen haka ne don zamani. Ko kuma mutumin da ya ceto wani a cikin rafi daga halaka, matukar ruwa bai shigan mai ba; azuminsa na nan.

Mutumin da ya wayi gari da janaba bai samu damar yin wanka kafin fitowar alfijir ba, shi ma azuminsa yana nan bai baci ba. Haka nan mutumin da ya ci abinci, ya sha abin sha bisa mantuwar cewa yana azumi, shi ma azuminsa bai karye ba. Manzon Allah (SAW) ya ce “Allah ne ya ciyar da shi, ya shayar da shi”, (amma ban da wanda ya ci da ganganci).

Amma a Mazhabarmu ta Malikiyya, Imam Malik ya ce “Idan mutum ya yi haka ne da Azumin Ramadan zai rama wannan azumin bayan sallah, idan kuma azumin nafila ne ba zai rama ba.” Sai dai kuma malamai solar ce wannan fatawar ta ramuwa da Imam Malik ya bayar kokarinsa ce, amma ba dole ne sai mutum ya rama ba.

Mutumin da ya sanya kwalli a idonsa azuminsa bai karye ba musamman idan kwallin na magani ne. A karkashin wannan, malamai solar ce mai azumi zai iya sanya magani a idonsa ko kunnensa idan suna ciwo kuma azuminsa bai karye ba koda ya ji dacin maganin a makwogoro, bisa hujjar cewa “duk abin da ba a shigar da shi ta kofar al’ada ba, ba ya karya azumi matukar lalura ce ta sanya yin hakan.”

Ita ma allura ba ta karya azumi koda an ji dacinta a makwogoro. Yin kaho, da diban jini daga jikin mutum ko kara wa mutum jini duk ba su bata azumi. Yin kurkurar baki, da shakar ruwa, (ba da yawa ba), da hadiyar yawu, da shakar kurar hanya ko kuda ya shige wa mutum baki ko hanci bai iya karewa ba; duk ba su karya azumi.

Idan gari ya shiga hancin mace mai yin tankade bai karya mata a zumi ba. Haka nan hadiyar kaki (majina) ko shafa man shafawa (ciki har da su rob da mantaleta ko taiga), da shafa turare ko kunna turaren wuta duk ba su karya azumi, sai dai Malikiyya ta kyamaci abin in dai ba bisa lalura ba.

Har ila yau, idan mutum ya sumbanci iyalinsa azuminsa bai baci ba. Wani ya tambayi Annabi (SAW) cewa “Idan mutum ya sumbanci iyalinsa azuminsa ya karye?”. Annabi (SAW) ya ce ma sa “Idan mutum ya kuskura baki azuminsa ya karye?” ya ce “a’a”, sai Annabi (SAW) ya ce “to ai shi kenan wancan ma bai karye ba”. Amma duk wanda ya san idan ya yi sumba (kiss) wani abu da zai sa shi keta haddi zai iya faruwa; ya kiyaye kar ya yi.
Fitar maziyyi ma bai karya azumi, illa kawai mutum ya yi tsarki. Haka nan idan wahala ta sanya mutum fitar da maniyyi azuminsa yana nan. Yin amai ba ya karya azumi (wasu malamai solar ce idan aka jawo aman da gangar ya karya).

Wadannan su ne abubuwan al’ada da idan aka yi ba su karya azumi. Mun mayar da hankali a kansu ne saboda solar fi rikitarwa a kan wadanda suke batawa kai tsaye da aka san su kamar ci da sha da ganganci, da saduwa da iyali da sauran su ko kuma mutum haka kawai ma ya ce shi ya fasa azumin, wannan azuminsa ya baci saboda ba a wasa da sha’anin Allah.

Za mu dakata a nan sai Allah ya kai mu mako mai zuwa. Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadiy wa ala alihi hakka kadirihi wa mikdarihil aziym.

What's On Your Mind?