Daukar Niyya Da Matakan Da Ba A Taba Ganin Irinsu Ba, Don Kafa Makomar Bai Daya Ta Bil’dama Da Halittu

0
77

Daukar Niyya Da Matakan Da Ba A Taba Ganin Irinsu Ba, Don Kafa Makomar Bai Daya Ta Bil’dama Da Halittu

A yau Alhamis, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci taron koli kan yanayi ta hanyar bidiyo daga nan Beijing tare kuma da gabatar da muhimmin jawabi.

A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, a yayin da ake tinkarar matsalolin da ba a taba ganin irinsu ba a harkokin kula da muhalli a duniya, ya kamata kasashen duniya su kudiri niyya tare da daukar matakai, da dauki nauyi don kafa makomar bai daya ta bil’adama da halittu.
Ya ce, wajibi ne mu kiyaye halittu da yanayin muhalli kamar yadda muke kiyaye idanunmu, tare da fito da wani sabon tsarin daidaito tsakanin bil’adama da halittu.
Xi Jinping ya nuna cewa, kyakkyawan muhalli shi ne tushen bunkasuwar tattalin arziki. Kare muhalln halittu yana nufin kare karfin samar da kayayyaki, kuma kyautata mahallin halittu yana nufin raya karfin samar da kayayyaki.
Baya ga haka, Xi Jinping ya nuna cewa, kasar Sin ta shigar da ra’ayin kiyaye muhallin halittu da raya irin ra’ayin a cikin Tsarin Mulkin Jamhuriyar Jama’ar Sin, tare da shigar da su cikin tsarin gurguzu mai halin musamman na kasar Sin. Kana da tsayawa kan hanyar ba da muhimmanci ga kiyaye muhallin halittu, da hanyar samun bunkasawa ba tare da gurbata kiyaye muhalli ba.
Xi Jinping ya kara da cewa, a shekarar da ta gabata, a hukumance ya sanar da cewa, kasar Sin za ta himmatu wajen ganin ta samu nasarar rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli nan da 2030, ta kuma daina fitar da shi baki daya ya zuwa 2060. Tsawon lokacin da kasar ta ke bukata wajen cimma burinta na rage fitar da hayaki mai gurbata muhalli zuwa daina fitar da shi baki daya, bai kai na lokacin da kasashe masu ci gaba ke bukata ba, don haka, kasar Sin tana bukatar yin namijin kokari a wannan fannin.
Xi Jinping ya kuma nuna cewa, ya kamata kasashe masu ci gaba, su kara daura niyya da daukar matakai a wannan fannin, su kuma taimaka wa kasashe masu tasowa don inganta karfinsu na tinkarar sauyin yanayi.
Haka zalika, Xi Jinping ya nuna cewa, kasar Sin na maraba da dawowar Amurka cikin tsarin kula da yanayin sauyin yanayi na bangarori da dama. Yanzu haka Sin da Amurka photo voltaic fitar da “Hadaddiyar sanarwa recreation da tinkarar matsalar sauyin yanayi” ba da dadewa ba, kasar Sin na fatan yin kokari tare da kasashen duniya, ciki har da Amurka, don inganta tsarin kula da muhalli a duniya. (Bilkisu Xin)

What's On Your Mind?