Daso Ta Shiga Kwaryar Manya A Instagram, Inda Ta Samu Mabiya Miliyan Daya

- Advertisement -

A ranar Juma’a, 4 ga Yuni, 2021 fitacciyar jaruma Saratu Giɗaɗo (Daso) ta cika samun mabiya miliyan ɗaya a Instagram.

Cikin murna ta bada sanarwar hakan a shafin ta na Instagram.

A saƙon nata wanda mujallar Fim ta kwafo, jarumar wadda ta shahara a wasannin barkwanci a masana’antar Kanywood ta ce, “A daɗe ana yi sai gaskiya. Alhamdulillah. Yau wayoyin ku sai sun cika da hotunan murnar samun mabiya miliyan ɗaya a shafi na na Instagram.”

Samuwar shafukan sada zumunta da muhawara na zamani irin su Facebook, Twitter da Instagram ta kawo sauye-sauye a fannoni da dama na rayuwar ɗan’adam.

Haka kuma shafukan sun kawo sauyi a yadda ake kasuwanci da neman ilimi da samun labarai da ma ‘tsegumi’.

Hakan ne ya sa ‘yan fim na Hausa su ka riƙi waɗannan shafuka wajen ganawa da masoyan su.

Akasarin ‘yan wasan na yin amfani da Instagram ne saboda kasancewar ta wani dandali da ake wallafa hotuna da bidiyo, wanda da ma shi ne burin masu sana’ar fim.

Yanzu Daso ta bi sahun fitattun jaruman Kannywood masu mabiya miliyan ɗaya zuwa sama, irin su Hadiza Gabon, Rahama Sadau, Ali Nuhu, Hafsat Idris, Ali Jita, Nafisat Abdullahi, da sauran su.

Ɗaruruwan masoyan ta sun taya ta murna saboda wannan kaiwa gaci da ta yi.
a lokeshin.

- Advertisement -