Darektar WTO: Neman Dakushe Sin A Fannin Gyare-Gyaren Ciniyayya Ba Zai Yi Nasara Ba

0
75

Darektar WTO: Neman Dakushe Sin A Fannin Gyare-Gyaren Ciniyayya Ba Zai Yi Nasara Ba

Daga CRI Hausa

Babbar darektar kungiyar cinikayya ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, ta bayyana cewa, kasar Sin za ta so ta shiga tattaunawar yiwa harkokin cinikayyar duniya gyare-gyare, idan har za a aiwatar da wannan manufa ba tare da neman dakushe sauran kasashe ba.
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito babbar darektar kungiyar na bayyana haka, yayin wani taro da hukumar gudanarwar tarayyar Turai ta shirya a ranar Litinin din da ta gabata.
Rahoton ya ce, Amurka da kungiyar EU da Japan, suna kokarin ganin an dakile rangwamen da kasashe ke baiwa masanaantu, don magance damuwar da ake nunawa kan kamfanonin mallakar gwamnatin kasar Sin.
Sai dai kuma, shawarar da suka gabatar na bukatar amincewar dukkan mambobin kungiyar WTO. Jagoran kungiyar, na duba yiwuwar tattaunawar da ta yi da kasar, a matsayi mai muhimmanci. Tana mai cewa, kasar Sin ta kara daukar matakai, idan har ta ga WTO ta magance wasu nauoin rangwame.
Kasar Sin ta bayyana cewa, a shirye ta ke ta tattauna batun rangwamen masanaantu, idan har aka fafada rangwamen zuwa bangaren aikin gona da ake bayarwa a kasashen yamma.(Mai fassarawa: Ibrahim daga CRI Hausa)

What's On Your Mind?