Darakta Falalu Dorayi Yayi Martani Kan Abinda Dr Gummi keyi akan Yan Ta’adda

0
86

A yau ranar juma’a falalu dorayi yayi kalamai masu dadi da yabon gwarzon malamin nan Dr Ahmad Gummi akan yan ta’adda ya wallafa hakan a shafinsa na sada zumunta.

“Malam Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi.

Yana namijin kokari akan sha’anin tsaro a yanki arewa.

Duk mai bin kafar zamani, zai yadda yake shiga tsakanin fulani yana basu kwarin gwiwa akan yadda Addini musulunci yace a yi zamantakewa. Tare da tsawatar da wasu matasa akan yinkurin da suke na shiga sawun masu laifi.

Darakta Falalu Dorayi Yayi Martani Kan Abinda Dr Gummi keyi akan Yan Ta’adda

Hotuna – Dr Gumi: Wa’azi A Dokar Daji !!Dr Gumi, Shehu Buba Kun Cancanci Yabo

Wannan kiran bude ido ne ga mahukunta, Yan siyasa, malamai da sarakuna da masu unguwa.

Bin irin turbar da ya samar, taimako ne garemu arewa.
Tabbas ina da yakenin in za’a bi ta sau da kafa kamar yadda ya fara.
In shaa Allah za’a magance 80% na rashin tsaro, ba tare da zubar da jini ba.

Nayi Imani babu abin da nasihar magabata ta bari.

Allah ya saka masa da alkairi.
Ya kara haske da albarka a cikin rayuwar sa. Ya kare shi. Amin.

[email protected] #brothers & #sisters

#falaludorayi
#falaluaforayi.”

What's On Your Mind?