Dangantakar Tattalin Arziki Da Al’adu Tsakanin Sin Da Saliyo Ta Kara Zurfi Cikin Shekaru 50 Da Suka Gabata

0
51

Dangantakar Tattalin Arziki Da Al’adu Tsakanin Sin Da Saliyo Ta Kara Zurfi Cikin Shekaru 50 Da Suka Gabata

Daga  CRI Hausa

Shugaban majalisar dokokin kasar Saliyo Abass Bundu, ya ce dangantakar tattalin arziki da al’adu tsakanin Sin da Saliyo, ta kara zurfi cikin shekaru 50 da suka gabata.

Abass Bundu ya bayyana haka ne yayin wani taron karawa juna sani da ofishin jakadancin Sin dake Saliyo ya shirya da hadin gwiwar kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dokokin kasar Saliyo da kuma kungiyar ‘yan jarida ta Saliyo.
Shugaban majalisar ya jaddada cewa, dabarun ci gaban tattalin arzikin Sin darasi ne ga kasar ta yammacin Afrika, yana mai cewa Saliyo na da karfin cimma nasara kamar kasar Sin bisa taimakon irin wadannan dabaru.

A bana ne ake cika shekaru 50 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Saliyo.

A nasa bangaren, Jakadan Sin dake Saliyo Hu Zhangliang cewa ya yi, shekaru 50 din da suka gabata, solar shaida cewa Sin da Saliyo aminai ne na kwarai da suka samu kwararan sakamako.

Ya ce kasar Sin ta taimakawa kasar Saliyo a lokacin da take fuskantar kalubale kamar na barkewar Ebola a shekarar 2014 da zaftarewar laka a shekarar 2017 da kuma annobar COVID-19 da ake fama da ita yanzu haka.

Har ila yau, ya ce ita ma Saliyo ta ba Sin goyon baya cikin wadancan shekaru, yana mai cewa, ta kasance mai taka rawa cikin dandalin hadin gwiwar Sin da Afrika na FOCAC, kana ta ba da gudunmuwa wajen raya dandalin. (Fa’iza Msutapha)

What's On Your Mind?