Dan Wasan Mafi Tsada A Kano Ya Mutu

0
34

A ranar Talata ne Ibrahim Salisu da ake kira Iriyos wanda aka saya mafi tsada a  garin Gano, dake a  karamar hukumar Dawakin Kudu a Kano ya mutu bayan da dan wasan ya yi fama da rashin lafiya daga baya ya ce ga garinku nan kuma tuni aka binne shi kamar yadda addinin musulunci ya tanada.

Sama da kaka daya kenan gidan radio BBC suka kawo labarin dan wasan, wanda kungiyar kwallon kafa ta Super Stars ta dauki Salisu Iriyos a matsayin mafi tsada a garin kuma ya fara buga wasa a kungiyar.

Dan Wasan Mafi Tsada A Kano Ya Mutu

Kuma Super Stars mai buga rukuni na biyu a gasar hukumar kwallon kafa ta jihar Kano ta sayo dan kwallon ne daga kungiyar kwallon kafa ta Aston Billa ta garin na Gano kan kudi naira dubu biyar daidai da fam 10.86.

Matashi ne mai cike da burin ya habaka wasanninsa da fatan wakiltar Gano da jihar Kano da Najeria a wasanninta nan gaba sannan dan wasa ne dogo mai cin kwallo a raga wanda ya bayyana alfaharinsa kan yadda yake cin kwallo idan ya shiga fili.

Masana kwallon kafa a garin na gano dai photo voltaic bayyana dan wasan a matsayin wanda nan gaba zai iya zama shahararren dan wasan gaba wanda duniya za tayi alfahari dashi duba da irin yadda yake zura kwallo  araga idan har aka kawo kwallon ko kuma yaje ya karbo da kansa.

A farkon makon Satumbar shekarar 2019 aka rufe kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallon kafa ta nahiyar Turai, musammam Italiya da Faransa da Jamus da kuma Spaniya wadanda sune manyan gasannin da ake ji dasu a duniya.

Ina Son Kafa Tarihi A Manchester City, Cewar Sabon Dan Wasa Dias

A nahiyar Afirka akan gudanar da cinikayyar ‘yan kwallo sai dai kudin da ake sayen dan kwallo ko kusa ba ya kai wadanda ake yi a Turai sannan a Najeriya ma an gudanar da wani ciniki mafi tsada a arin Gano da ke karamar hukumar Dawakin Kudu, inda Super Stars ta dauki Ibrahim Salisu Iriyos a matsayin mafi tsada a garin a wancan lokaci.

Super Stars mai buga rukuni na biyu a gasar hukumar kwallon kafa ta jihar Kano ta sayo Ibrahin Iriyos daga kungiyar kwallon kafa ta Aston Billa itama wadda take a garin na Gano kan kudi naira dubu biyar daidai da fam 10.86.

Dan wasan mai cin kwallo shi da kansa ya yi sha’awar komawa Super Stars da buga wasa ganin tana mataki na sama fiye da kungiyarsa ta Aston Billa Gano inda nan da nan suma shugabannin na Super Stars suka kai tayin kudi kuma aka sayar musu.

Hakan ya sa Iriyos kan je Super Stars atisaye a lokacin da kungiyarsa Aston Billa ke yin hutu, wanda hakan ya sa nan da nan aka amince da yadda yake buga wasa aka kuma cimma matsaya a dauko shi.

Idin Gano shi ne shugaban kungiyar kwallon kafa ta Super Stars wanda ya je wajen kocin Aston Billa, Abba Alasan Isa wanda ake kira Abba Goma suka cimma matsaya kan farashin Ibrahim Iriyos akan naira dubu biyar.

Haka kuma Watford ta kulla yarjejeniyar daukar matashi dan shekara 17, mai buga wa tawagar Guinea kwallo, Djibril Toure daga Ceffomig FC, kan kwantiragin shekara biyar da rabi kuma zai kammala komawa kungiyar daga ranar 1 ga watan Janairun shekara ta 2021 mai zuwa.

What's On Your Mind?