Dan Kwangila Ya Samu Lambar Yabo Bayan Da Ya Yi Wa Bauchi Tukuicin Azuzuwan Karatu 2 Kyauta

0
116

Dan Kwangila Ya Samu Lambar Yabo Bayan Da Ya Yi Wa Bauchi Tukuicin Azuzuwan Karatu 2 Kyauta

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

 

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya nuna jinjinarsa ga kamfanin ‘BashDee Transport Restricted’ bisa gudanar da nagartacce kuma ingantaccen aikin gina dakunan da gwamnatin ta baiwa kamfanin kwantiragin aiwatarwa.

 

Sannan, gwamnan ya nuna yabonsa ga dan kwangilar bisa tukuicin azuzuwa biyu da ya gina wa gwamnatin jihar kyauta domin nuna godiya da kwangilar da gwamnatin ta baiwa kamfaninsa, Bala ya bayyana cewar tabbas irin wadannan ‘yan kwangilar ake nema a Nijeriya domin kishinsu ga ci gaban kasa.

 

Gwamnan ya karrama dan kwangilar ne a yayin kaddamar da rabon kayan karatu na shirin BESDA wanda ya gudana a makarantar Firamaren sojoji da ke Bauchi.

 

Bala, ya bayyana cewar tabbas dan kwangilar ya cancanci yabo domin kuwa ya gina wasu karin azuzuwa biyu a kan guda uku da aka ba shi kwantiragin ginawa, don haka ne ya nuna cewa tabbas yin hakan ya nuna irin gudunmawar da ya bayar wajen inganta harkar ilimi a jihar.

 

Kan wannan matakin, gwamnan ya bayyana cewar tabbas gwamnatinsa za ta ci gaba da yin aiki tare da kamfanin BashDee Transport Restricted wajen gudanar da ayyuka da tsare-tsaren gina azuzuwa domin tabbatar da kai azuzuwan daukar darasi zuwa matakin da ya dace a jihar.

 

Ya ce: “A madadin gwamnati da al’umman jihar Bauchi, ina mika takardar jinjina wa Manajin Darakta na kamfanin BashDee Restricted bisa gudanar da aikin tallafi da ya mana. Mun ga irin kyakkyawar aikin da dan kwangilar ya yi na gina wasu karin azuzuwa biyu daban da wanda muka ba shi kwangilar yi.

 

“Abun da ka yi tabbas na yi imanin shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi alfari da kai saboda irin ‘yan kwangilar da muke nema kenan a Jihar Bauchi da ma Nijeriya baki daya.”

 

Gwamna Bala Muhammad ya bada tabbacin gwamnatinsa na cigaba da aiwatarwa da gudanar da nagartattun ayyukan bunkasa ilimi daidai da tsarin kai ilimi zuwa babban mataki, yana mai kiran masu ruwa da tsaki da su dafa wajen cimma wannan nasarar da aka sanya a gaba.

 

Da ya ke maida jawabinsa, Manajin Darakta na kamfanin BashDee Transport Restricted, Alhaji Bashir Isah, ya nuna matukar godiyarsa ga gwamna Bala Muhammad a bisa yabon da aka masa, yana mai cewa tabbas hakan zai kara wa kamfaninsa kumajin cigaba da yin aikin taimako a kokarinsu na bada gudunmawa ga cigaban al’umma.

 

Bashir Isah ya yi bayanin cewa kamfaninsa ya dauki matsayar gina wasu karin azuzuwa biyu wanda bai daga cikin yarjejeniyar da suka cimma da gwamnatin ne domin ya zama tukuici ga sakayayar basu kwangila da gwamnan jihar ya yi, ya ce a shirye suke su cigaba da bada gudunmawa domin dafa wa kokarin gwamnati mai ci.

What's On Your Mind?