Dan kwallon Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da ginin katafaren makaranta a Jos

0
39

Kyaftan na Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da shirin ginin katafaren makaranta a Bukuru, karamar hukumar Jos South ta jihar Plateau saboda a wajen ya girma.

Ahmed Musa ya bayyana cewa zai gina makarantan ne matsayin mayar da alherin da garin tayi masa a matsayin mahaifarsa.

Dan kwallon Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da ginin katafaren makaranta a Jos

A sako mai kama da martani a shafinsa na Tuwita, Ahmed Musa, ya ce bai jahilci bukatar yin hakan ba.

“Ban jahilci bukatar mayar da alheri garina ba kuma dalilin haka ya sa nike farin cikin sanar da kaddamar da ginin makarantar M & S Worldwide College a jihar Plateau, karamar hukumar Jos ta kudu Bukuru,” ya ce.

Dan kwallon Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da ginin katafaren makaranta a Jos

Dan kwallon Super Eagles, Ahmed Musa, ya kaddamar da ginin katafaren makaranta a Jos

Gwamnatin Shugaba Buhari zata ari kudin mutane dake ajiye a banki basa amfani dasu

Musa ya zama kyaftan din Super Eagles bayan John Obi Mikel yayi ritaya.

Ahmed Musa ya taka leda a kasashe irinsu Rasha, Holland, Ingila, da Saudiyya.

A wani labarin kuwa, Ahmad Musa, ya bayyana shirinsa na bude wani katafaren flin wasanni a cikin birnin jihar Kaduna.

Tsohon dan wasan CSKA Moscow da Al Nasr na Sadiyya ya bayyana bidiyon wurin kuma da alamun an kusa kammalawa.

Wannan na zuwa ne shekaru biyu bayan wata daya bude a Kano, yayinda kuma ya bude shagon aski na alfarma bayan haka.

An gina filin ne a yalwataccen fili kuma za’a iya wasannin waje da na kulle.

What's On Your Mind?