Dan Again Izala Ba sujjada Yayi Ba 

- Advertisement -


Daga Tatti Assalafi.
Wasu mutane suna ta yada wannan hoton cewa ‘dan agaji na kungiyar Izala ya yiwa Sheikh Bashir Nyandu sujjada yana gaishe shi.

Magana ta gaskiya ‘dan agajin Izala bai yiwa Malam Bashir sujuda ba, kuma ba gaisuwa yake yiwa Malamin ba.

Dan agajij izala yana atisaye ne wato press-up domin ya nunawa Sheikh Bashir jarunta irin na ‘dan agaji, wannan shine gaskiyar abinda ya faru.

Dan agajin sai da suka gaisa hannu da hannu da Malamin a tsaye, kafin yaje kasa yayi press-up kamar yadda sojoji suke yi.

Allah Ka taimaki Musulunci da Musulmai.

- Advertisement -