Dalilin da ya sa nake gayyatar Kiristoci masallaci wurin tafsiri da Ramadan – Sheikh Khalid

0
51

An haifi Sheikh Muhammad Nuru Khalid a ranar 1 ga watan Oktoban 1960, wato ranar ɗaya da aka bai wa Najeriya ƴancin kai kenan.

An haifi malamin a cikin garin Jos, jihar Filato, kuma a garin na Jos ɗin ne malamin ya tashi kuma ya yi rayuwarsa.

A tattaunawar da BBC ta yi da malamin, ya bayyana cewa zai yi wuya ya iya tantance lokacin da ya fara karatu, domin mahaifinsa malami ne, don haka ya tsinci kansa ne cikin karatu.

Sheikh Nuru ya bayyana cewa ya haddace Al-Qur’ani tun yana ɗan ƙaramin yaro a gaban mahaifinsa.

Sai dai duk da cewa mahafin Sheikh Nuru malami ne, hakan bai hana shi zuwa wurin sauran malamai ba domin ɗaukar karatu.

Malamin ya shaida wa BBC cewa yana da mata huɗu da ƴaƴa 28 da jikoki 10.

Gwagwarmayar karatu

Daga cikin malalan da ya yi karatu a wurinsu akwai wani Malami da ake kiransa Malam Na Rogo, sa’annan akwai Malam Baban Makaranta akwai kuma Malam Kawu, wandA a wurinsa ne Sheik Nuru ya rinƙa zuwa ɗaukar karatu da dare da kuma koyon ƙasidodi irin na Maulidi.

Sheikh Nuru ya bayyana cewa kafin a saka shi makarantar boko, sai da aka saka shi makarantar allo wurin wani Malam Tijjani, ya yi almajiranci da kuma bara kamar yadda kowane almajiri yake yi.

Sai dai a hirar da BBC ta yi da Sheikh Nuru, ya yi bayani matuƙa dangane da irin gudunmawar da Malam Bawa Mai Shinkafa ya bayar a rayuwarsa, inda ya ce saboda zaman mutuncin da suka yi har Malam Bawa ya bai wa Sheik Nuru ƴarsa ya aura, kuma yanzu suna da ƴaƴa biyar da ita da kuma jika ɗaya.

A bangaren karatun boko kuma, malamin ya fara ne daga makarantar firamare a cikin garin Jos.

Ga bidiyon tattaunawar malam kenan da BBC Hausa.

Ya ce Allah bai ƙaddara ya je sakandare ba saboda rashin ƙarfi, amma daga baya ya shiga wata makaranta ta Izala ta Faculty For Greater Islamic inda ya ci gaba da karatun boko.

Daga baya ya samu ya zana jarabbawa ta GCE da Jamb inda ya samu gurbin karatu a jami’ar Jos inda ya yi karatun digiri ɓangaren ilimin Addinin Musulunci.

Komaar Sheikh Nuru Khalid Abuja

Sheikh Nuru Khalid ya bayyana cewa tun da farko mutanen Nyanya da ke Abuja suka je Jos wurin Sheikh Bawa Mai Shinkafa inda suka ce suna neman wanda zai rinƙa koya musu karatu.

Hakan ya sa Sheikh Bawa ya ce ya je ya gani idan zaman zai yiwu sai ya karantar da su a can, wanda hakan ya sa Sheikh Nuru ya koma Abuja.

Daga baya kuma sai aka buɗe wani masallacin Juma’a a Karu sai Sheikh Nuru ya koma can yana limanci inda ya shafe wata tara a wurin.

Bayan nan ne aka kuma neme shi ya zo ya riƙe masallacin ƴan majalisu da ke Unguwar Apo a Abuja, inda a nan ne malamin ya shahara har duniya ta san shi.

Dalilin Sheikh Nuru na amfani da kwamfuta a wurin wa’azi

Sheikh Nuru Khalid ya bayyana cewa tun yana a Nyanya ya fara amfani da kwamfuta a wurin wa’azi, amma ko da ya je masallacin Apo ya ga akwai ƴan boko da ƴan siyasa da dama sai ya juya akalar wa’azinsa ya koma gaurayawa da Turanci kuma ya ƙarfafa amfani da intanet da kuma kwamfuta.

Ya shaida mana cewa hakan ya sa yaransa suka fara cewa “baba fa digital ne”, hakan ne ya sa aka fara yi masa laƙabi da Digital Imam.

Fannin da Sheikh Nuru ya fi ƙwarewa a kai

Sheikh Nuru Khalid ya shaida mana cewa babu wani fanni ɗaya da zai iya cewa ya fi ƙwarewa a kai, ko Hadisi ko Al-Qur’ani ko Tauhidi.

A cewarsa, shi har yanzu ɗan koyo ne amma kuma inda ya fi mayar da hankali shi ne ilimin shari’a, “musamman haɗa hancin shari’a da falsafa”, kamar yadda ya shaida mana

Dalilin Sheikh na gayyatar Kiristoci Masallaci da azumi

A duk lokacin da Sheikh Nuru Khalid ke tafsir a lokacin azumin watan Ramadan, akan ga ya gayyato Kiristoci wurin tafsirin.

A tattaunawar da ya yi da BBC, ya shaida cewa “na lura ana so a kunna wutar ƙiyayya da gaba tsakanin Musulmi da Kiritoci a Najeriya musamman arewaci, sai na ga cewa Manzon Allah (SAW) a masallacinsa Kiristoci da Nasara sukan zo ya zama shi ne a tsakiya yana yi musu bayani.

“Idan Manzon Allah Kiristoci za su shiga masallacinsa me ya sa ni ba za su shiga nawa ba,” in ji Sheikh Nuru.

What's On Your Mind?