Dalilan Da Suka Sa Maza Suka Fi Mata Saurin Mutuwa

Dalilan Da Suka Sa Maza Suka Fi Mata Saurin Mutuwa

Abu uku ne ke tasiri a kan yawan mutane, bayansu kuma babu cikon na hudunsu. Na farko akwai mutuwa, haihuwa sannan kuma hijira.

A wannan makon zan so ne mu shiga cikin mutuwa tare da fahimtar alakarta da yawan al’umma (Inhabitants). Masana tun a farkon wannan fanni na ilmin kimiyyar yawan al’umma ‘Demography’ photo voltaic fara yin bayanai ne dangane da mutuwa, bisa dalilin cewa ita mutuwa barazana ce ga yawan al’umma, ba ta kara yawan mutane, sai dai ta rage su.

Saboda wancan dalili ne masanan suka ba al’amarin mutuwa muhimmancin gaske, suka yi ta gudanar da binciken musamman domin a iya fahimtar MUTUWA da irin gudummawar da ta ke bayarwa ga raguwar al’umma.

Mutuwa dai dole ce, babu wata halitta da ta isa ta yi fariyan cewa ita da mutuwa photo voltaic raba gari. Kowanne mutum yana da alaka da mutuwa, ko don wannan alakar ta musamman da ke tsakanin mutane da mutuwa, ya ishi masana halayyar jama’a da zamantakewa su yi bincike a kanta.

Wannan ba takaddama ba ce da aka fara a yau. An tafka muhawara sosai dangane da jinsin da ya fi saurin mutuwa tsakanin maza da mata, wanda saboda a kaucewa zargin bin son rai, gudun kaucewa matakan tabbatar da ilmi ya sa masana suka yi ta sabunta binciken.

Ban manta ba, na taba karanta muhawarar wani masani mai suna John Grunt a binciken ilmin da ya gudanar a shekarar 1662 a Landan. Ya gudanar da binciken ne ta hanyar bibiyan dukkanin ofisoshin rijistar mutuwa inda ya tattara bayanai dangane da adadin yawan matattun da a ke da su. Sakamakon binciken John Grunt ya yi nuni da cewa ‘An fi haihuwar Maza fiye da Mata; sannan kuma Maza photo voltaic fi mata saurin mutuwa’.

Irin wadannan bincike na suna nan da yawa wadanda masana suka gudanar tare da fid da sakamako. A wannan sharhin nawa, kafa misali da binciken John Graunt kadai ya wadatar, saboda idan zan ci gaba da kawo misalai ba zan samu damar dora wasu bayanai masu muhimmanci ba.

A dai dai lokacin da a ka haifi jariri daga shekara 0, a wannan shekarar babban abin da ya fi komi sauki shi ne ya kwashi kwayoyin cuta wadanda ke kashe garkuwan jikin dan Adam, saboda kwayoyin garkuwan jikin jariri ba su da kwari. Dalilin haka ne jarirai da dama ke kasa tsallake wannan shekara.

Mummunan Hatsarin Mota Ya Ci Rayukan Mutum 20 A Bauchi

Ko a tsakanin shekara ta 0 da a ke tsammanin yawaitar mutuwan jarirai sakamakon iya diban kwayoyin cuta; Maza photo voltaic fi mata diban wadannan kwayoyin cuta, kuma photo voltaic fi mata mutuwa a lokacin da suke Jarirai.

Dalilin da ya sa Maza suka fi Mata fuskantar barazanar mutuwa a shekarar da suke Jarirai shi ne; Mace Allah ya na halittarta ne da wasu kariya na musamman, wanda Namiji ba shi da su, wanda wadannan kariya na musamman da ke kumshe a jikinsu ne ke yi musu garkuwa da dukkan cututtukan da ke kashe garkuwan jiki.

Daga shekarar haihuwa sifili zuwa hudu; daga shekara hudu sannan garkuwan jikin jarirai ke samun kuzarin da ya kamata, don haka babu fargabar za su iya arba da kwayoyin cutan da ka – iya zama sanadiyyan rasa ransu.

Saboda haka bayan nazari da binciken masana, lissafi ya tantance cewa daga shekara 15 zuwa sama Maza photo voltaic fi mata mutuwa, sannan photo voltaic fi Mata kasancewa a cikin hadurran da ka iya cinye rayukansu.

Dalili a nan shi ne, Maza suna fara ayyuka da sana’o’in da za su rika barazana ga rayukansu, barazana ga garkuwan jikinsu, barazana ga dukkan wani tattali da su ke yi na kiwon lafiya. Irin wadannan ayyyuka photo voltaic hada da aiki a masana’antu, ma’adinai, masarrafa da sauransu. Misali, ya za ka kwatanta garkuwar jikin mutumin da ke aiki a ma’aikatar da a ke amfani da sinadarin ‘Chemical substances’, wanda shakarshi babban hadari ne ga rayuwa.

A wani bincike kwanan nan, wani bawan Allah mai sana’ar siyar da tabarma ya sanar da ni cewa; ya gano cewa dukkanin masu aiki a masarrafan tabarmu ba su jimawa su ke mutuwa, sakamakon sinadarin ‘Chemical’ din da su ke shaka.

A nan akwai takaddama babba, amma takaddamar na tasowa ne kadai a Nijeriya da wasu kasashen da a ke kira da ‘kasashe masu habbaka’. Takaddamar ita ce; a kasashen da su ka ci gaba babu barazanar mutuwa ga Mata masu juna biyu, saboda su na kiyaye duk wata ka’ida ta likitoci, sannan kuma akwai kwararru da asibitocin wadatattu.

Amma idan mutum ya kwatanta da irin kasarmu Nijeriya, zai ga cewa Mata photo voltaic fi rasa ransu a lokuta da dama yayin da su ke dauke da juna biyu. Don haka a nan za mu iya kawo cewa a shekara 15 zuwa 49 Mata a kasarmu su na fuskantar yiwuwar haduwa da mutuwa, saboda ba a basu kulawar da ta dace.

Daga shekara 49 zuwa sama, a wannan lokacin kuma garkuwan jiki ta fara yin rauni, don haka ko a sannan Maza photo voltaic fi mutuwa fiye da Mata, saboda har zuwa wannan lokacin kariyar musamman da suke da ita daga Allah ba ta rabu da su ba.

Daga karshe, zan so mai karatu ya san cewa wannan nazari ya ginu ne bisa tabbatattun hujjojin da a ke dasu, wadanda a ka samu bayan an gudanar da binciken kimiyya ‘Evaluation’ tare da kiyaye ka’idojin binciken.

Mu hadu mako mai zuwa!

 915 total views,  6 views today

About M. Jamiu 1373 Articles
Muhammed Jamiu is a Head Editor at Mobilized9ja (M9JA). He has been publishing for 8 years and focused more on Local/World News, Nigeria Music & Video all in English and Hausa Language.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*