Dalilan Da Ke Sawa Ana Haihuwar Bebaye

- Advertisement -

Dalilan Da Ke Sawa Ana Haihuwar Bebaye

Daga Idris Aliyu Daudawa,

Dokta Constanza ta nemi a rinka koyar da harshen bebaye a makarantu

Dr. Halima ‘Yar Fulani wadda Bajamushiya ce da take aiki a wata jami’a da ke kudancin kasar Jamus, ta bayyana cewa akwai dalilan da ke sanyawa a haifi mutum da larurar bebantaka.

Dokta Halima da ke nazari kan harshen Hausa ta bayyana cewa, “akwai dalilai masu yawa da ke sawa mutum ya zama bebe ko a haife shi bebe musamman ma idan uwa ta sha wani magani lokacin da take dauke da juna biyu. Sannan kuma cutar sankarau na daya daga cikin cututtukan da suke sanadiyar kamuwwa cutar ta bebantaka.”

Majalisar dinkin duniya da ta ware ranar 23 ga watan Satumbar kowacce shekara, domin tunatar da al’umma da sauran masu ruwa da tsaki wajen fahimtar irin bukatar da ake da ita ta wajen fadada harshen bebaye domin su ma a rika tafiya tare da su.

 

Hakan ne ya sa Dokta Halima ta ce “wannan rana ta harshen bebaye na da muhimmanci sosai saboda dalilai guda biyu: tana sanar da mu cewa harshen bebaye harshe ne na ainahi wato kamar sauran harsunan duniya yake misali kamar Laribci ko Turanci ko kuma Hausa.

 

Har ila yau kuma ranar tana tunatar da mu irin hakkin da bebaye suke da shi na yin amfani da harshensu.”

Halima ‘yar Fulani ta kuma bayyana bukatar da ake da ita ga likitoci da lauyoyi da sauran kwararru wajen fahimtar harshen bebaye domin samun damar tattaunawa da su lokacin da bukatar hakan ta taso.

 

To sai dai masaniyar harshen na bebaye ta kara da cewa “amma abin da ya fi shi ne a koyar da harshen bebaye a jami’a da kuma tafinta domin samun mutanen da za su iya yin aikin tafinta a duk wuraren da ake bukatar su ko a asibiti ko a kotu koma a jami’a.”

Hakan a cewar Dokta Halima “zai bai wa bebaye damar yin karatu har zuwa matakin digiri domin zama likita ko lauya da sauransu.”

 

Ko me ya sa bebaye ba sa son hulda da sauran jama’a?

Akwai dalilai da yawa da ke sa mutum ya zama bebe ko a haife shi bebe, musamman ma idan uwa ta sha wani magani a lokacin da take da juna biyu.”

Dokta Contanza Halima Shamailing
Malama a wata jami’a da ke kudancin kasar Jamus

Mafi yawancin lokaci, bebaye kan kasance tare da junansu domin tattaunawa, inda a wasu lokutan ma a kan samu yanayin da bebaye kan bar gidajensu domin zuwa wurin ‘yan uwansu bebaye.

Dokta Halima ta ce “ka taba zuwa kasar da ba ka jin yarensu? To su bebaye haka suke saboda haka ai babu mamaki domin bebe ya tafi wurin sauran bebaye domin su tattauna.

 

Amma akwai mutanen da ke jin harshen na bebaye musamman a kauyuka inda suke tattaunawa cikin harshensu wato maganar hannu.

Kuma solar koyi wannan yaren ne saboda ko dai suna da ‘yan uwa bebaye ko kuma makwabta ko kuma saboda suna sha’awar harshen na bebaye.”

 

‘Ayyukan da ta yi kan harshen bebaye’

 

Dokta Halima ‘Yar Fulani ta bayyana cewa ta yi ayyuka da dama tare da manufar inganta harshen bebaye inda kuma ta ce “mun riga mun yi litattafai guda takwas a fannoni daban-daban misali kasuwanci da lokaci.”

 

Yanzu dai malama Halima ta ce tana kan aikin littafi na 9 a fannin addini sannan kuma ta ce “ana iya samun dukkannin alamomi da rubutun bebaye a manhajar maganar hannu.”

 

Ta ce,”Akwai wadanda ke warkewa idan solar kamu da wannan lalura, kamar wadanda lakar tasu bata gama tsinkewa ba, to a kan yi masu aiki su kuma warke’.

Dakta Mamman Muhammad Lawal, ya bayyana cewa ga wadanda lakarsu ta yanke gaba daya, to a gaskiya su irin wadannan ba su warkewa.

Likitan ya kara da cewa, masu irin wannan lalura na matukar bukatar kulawa ta musamman, sannan kuma yakamata a samu jami’an lafiya da zasu rika basu shawarwari ta yadda za su rika kulawa da kansu da ma yadda za su koma harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata damuwa ba.

- Advertisement -