Dalibin Jami’ar Greenfield Ta Kaduna Ya Kubuta

0
71

Dalibin Jami’ar Greenfield Ta Kaduna Ya Kubuta

Daya daga cikin dalibai 22 da ‘yan bindiga suka sace a Jami’ar Greenfield dake kan hanyar Kaduna zuwa Abuja ya kubuta daga hannun ‘yan bayan shafe kwanaki. Wannan ya biyo bayan wa’adin da ‘yan bindigar suka bayar cewa in dai ba a cika kudin fansar nan ba, toh za su hallaka daliban.

Mahaifiyar dalibin ce ta tabbatar wa da manema labarai cewa danta ya kubuta. A yayin da iyayen sauran daliban suke ci gaba da rokon gwamnati da ta kubutar musu da ‘ya’yansu. ‘Yan bindigar solar bukaci miliyan 100, inda zuwa yanzu miliyan 55 kawai aka iya mika musu.

What's On Your Mind?