Dakunan Adana Kayayyakin Tarihin Sin Za Su Kara Karfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Kasa Da Kasa

- Advertisement -

Dakunan Adana Kayayyakin Tarihin Sin Za Su Kara Karfafa Hadin Gwiwa Tsakanin Kasa Da Kasa

Daga CRI Hausa

Yau 18 ga watan Mayu, rana ce ta dakin adana kayayyakin tarihi ta duniya. Babban taken ranar a bana shi ne, “makomar dakin adana kayayyakin tarihi: farfadowa da sake ginawa”.

Jami’an hukumar kula da kayayyakin tarihi ta kasar Sin solar fayyace cewa, dakunan adana kayayyakin tarihin kasar Sin, za su kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa, bayan kawon karshen annobar cutar COVID-19, ta yadda za su dakile kalubaloli iri daban daban, tare da dakunan adana kayayyakin tarihi a fadin duniya.

Babban taken ranar dakin adana kayayyakin tarihin duniya ta bana da kungiyar dakin adana kayayyakin tarihin duniya ta sanar shi ne, “makomar dakin adana kayayyakin tarihi: farfadowa da sake ginawa”, wanda aka gabatar bisa yanayin da daukacin kasashen duniya ke ciki, wato kokarin da suke yi domin kandagarkin yaduwar annobar COVID-19, tun daga bara wato shekarar 2020 da ta shude, saboda a karkashin irin wannan yanayi, ya dace dakunan adana kayayyakin tarihi dake fadin duniya su yi la’akari da batutuwan dake shafar yadda za su fuskanci kalubaloli, da yadda za su gyara, da kuma kyautata aikinsu, domin samun sabon ci gaba ta hanyar amfani da sabbin dabaru da sabon salo.

Mataimakin shugaban kungiyar dakin adana kayayyakin tarihi na duniya, kuma mataimakin shugaban kungiyar dakin adana kayayyakin tarihi na kasar Sin An Laishun, ya bayyana cewa, babban taken ranar dakin adana kayayyakin tarihin duniya na bana yana da babbar ma’ana, yana mai cewa, “Abu ne mai sauki a fahimci ma’anar farfadowa, wato maido da yanayin da dakunan adana kayayyakin tarihi na duniya suke ciki, a fannonin bude su, da harkar kudinsa da kuma amfaninsa. Recreation da ma’anar sake ginawa kuwa, ana iya cewa, akwai bukatar a sake gina kimar dakunan adana kayayyakin tarihi a idon al’ummun kasashen duniya. Kana ya dace a sake tsara fasalin gina dakunan adana kayayyakin tarihi, domin samun sabon ci gaba.”
Sabbin alkaluman da hukumar UNESCO ta fitar solar nuna cewa, a shekarar bara, matsakaicin tsawon lokacin da aka rufe dakunan adana kayayyakin tarihi a fadin duniya ya kai kwanaki 150, sakamakon yaduwar cutar COVID-19, kuma adadin kudin shigar da suka ragu ya kai kaso 40 zuwa 60 cikin dari. Ban da haka, rahotannin nazari guda biyu da hukumar UNESCO da kungiyar dakin adana kayayyakin tarihi na duniya suka fitar cikin hadin gwiwa a bara, solar nuna cewa, dakunan adana kayayaykin tarihi a fadin duniya kaso 90 cikin dari, solar rufe kofofinsu bisa matakai daban daban, bisa dalilin tasirin cutar. Har ma an yi hasashen cewa, a cikin dakunan, kaso 6 cikin dari ba za su bude kofa ba, kuma akwai wahala kaso 18 cikin dari su sake bude kofarsu.

Amma abun faranta rai shi ne, matsakaicin tsawon lokacin rufe kofe dakunan adana kayayyakin tarihin kasar Sin bai kai kwanaki 30 ba.
Mataimakin shugaban hukumar kula da kayayyakin tarihin kasar Sin Guan Qiang ya bayyana cewa, yanzu haka ana kokarin dakile yaduwar cutar COVID-19 a fadin duniya, har ya kasance aiki na yau da kullum. A don haka hadin gwiwar dake tsakanin dakunan adana kayayyakin tarihin kasa da kasa yana da muhimmanci matuka, saboda hakan zai ingiza cudanyar dake tsakanin wayewar kai iri daban daban a fadin duniya. A hannu guda kuma, zai taka rawar gani wajen gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya, a cewarsa: “Da farko dai, ya dace a kara karfafa aikin fasaltawa, da sulhuntawa, yayin da ake tsarawa, da kuma aiwatar da shiri na matsakacin lokaci, da na dogon lokaci, da shirin shekara shekara na baje kolin kayayyakin tarihi a ketare, ta yadda za a yi cikakkun nune-nunen al’adun al’ummun kasar Sin ga al’ummun kasashen duniya.

Na biyu, kamata ya yi a kara karfafa aikin yin bayani kan tunanin da’a, da al’adun gargajiya da kayayyakin tarihi suke nunawa, ta hanyar horas da ma’aikatan dake gudanar da aikin baje kolin, ta yadda za a yada wayewar kan al’ummun kasar Sin a fadin duniya yadda ya kamata.”
Guan Qiang ya yi nuni da cewa, a sabon zamanin da ake ciki, ya dace a yi amfani da dabarun kafofin watsa labarai na zamani, yayin dake ake yin cudanya tsakanin kasa da kasa, yana mai cewa, “Ya kamata mu kara karfafa amfanin kimiyya da fasaha ta zamani, da kuma cudanyar dake tsakanin bangarori daban daban. Misali a yi baje kolin kayayyakin tarihi a zahiri, da kuma ta yanar gizo, domin kafa tsarin yada wayewar kan al’ummun Sinawa, ta yadda za a kara habaka tasirin wayewar kan al’ummun Sinawa, da karfin yaduwarsa a fadin duniya.”(Mai fassarawa: Jamila daga CRI Hausa)

- Advertisement -