Dakta Zainab Bagudu Ta Bukaci ‘Yan Jaridu Su Karfafa Zaman Lafiya A  Nijeriya

- Advertisement -

Dakta Zainab Bagudu Ta Bukaci ‘Yan Jaridu Su Karfafa Zaman Lafiya A  Nijeriya

Daga Umar Faruk,
Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Dakta Zainab Shinkafi Bagudu, ta bukaci ‘yan jaridu a kasar nan, da su ci gaba da kokarin karfafa  zaman lafiya, hadin kai a tsakanin mutanen Nijeriya yayin gudanar da ayyukansu na jarida.

Dr. Zainab Bagudu ta yi wannan rokon ne a Birnin Kebbi, yayin  wata ziyarar da ‘yan jaridu suka kaiwa matar  a fadar gwamnatin a matsayin gaisuwar bikin Sallah.

A cewarta, yada labaran   farfaganda, kalaman kiyayya da labaran karya sune asalin kisan kare dangi da aka yi a kasar  Ruwanda da kuma wanda Hitler ya aikata.

“A halin da ake ciki,  yanzu a Nijeriya, wasu marasa kishin kasa na kokarin  raba kan ‘yan kasar da rusa ta kuma bai kamata a basu damar yin nasara ba.

‘Yan jarida a Jihar Kebbi da Nijeriya solar kasance masu kwazo da biyayya kuma ya kamata ku kara himma don sauya yanayin daga maras kyau zuwa mai kyau don kara samar da zaman lafiya ga kasa da mutanen ta.

“Ya kamata ku ci gaba da kokarin na fadakar da al’umma  don magance mummunan halin da ake ciki  na rashin zama lafiya, Saboda haka akwai bukatar kafafen yada labaru na kasar nan  su bunkasa hadin kai da  nuna kishin  kasar don kara samun zaman lafiya da kwanciyar hankali, in ji ta”.

Dokta Shinkafi  Bagudu ta kuma koka kan yadda ake amfani da kafafen sada zumunta kan yada labarun karya da kuma lalata sunan  kasar Nijeriya ga idon wasu kasashen duniya.

Ta lura cewa, mijinta, Sanata Abubakar Atiku Bagudu yana aiki ba dare ba rana, don gina jihar Kebbi da kasar Nijeriya baki daya.

Haka kuma Dakta Zainab Bagudu ta kuma sha alwashin ci gaba da kasancewa babban hadimin ci gaban tare da ‘Yan Jaridun kasar nan  don samar da  kyakkyawan suna ga Jihar Kebbi da Nijeriya baki daya.

Haka zalika  Matar Gwamnan ta bayyana watan Ramadana a matsayin lokacin zaman lafiya, tunani da walwala ga al’ummar kasar nan. Saboda a lokacin ne mutane da yawan ke sadaukar da kai wurin bautar Allah da kuma neman gafarawar Ubangaji Allah.

Mashawarci na musamman ga Gwamnan kan harkokin yada labarai, Yahaya Sarki, Shugaban kungiyar ’yan jarida na Jihar Kebbi NUJ, Alhaji Aliyu Jajirma, babban mataimaki na musamman ga Gwamnan kan kafafen sada zumunta, Aliyu Bandado, wanda  shi ne ya jagoranci ‘yan jaridu a lokacin da suka kai ziyarar Sallah ga Dakta Zainab Shinkafi Bagudu a Gidan Gwamnati, Birnin kebbi a jiya.

- Advertisement -