Dakarun rundunar sojin Najeriya sun ragargaji yan Boko Haram, sun kashe mutum 5

0
68

Hedlkwatar tsaro ta ce dakarun Operation Tura Takaibango sun halaka yan Boko Haram biyar a kokarinsu na ketare garuruwan Abbagajiri da Dusula da ke karamar hukumar Damboa na jihar Borno.

Birgediya Janar, Benard Onyeuko, mukaddashin darakta na ayyukan tsaro, a wani jawabi a ranar Juma’a, ya ce dakarun sun yi gagarumin nasara a kan yan ta’adda a arewa maso gabas.

Onyeuko ya ce dakarun tawaga ta musamman na 402 a ranar Laraba, sun gano tare da kewaye wasu yan bindiga a Abbagajiri sannan suka bude masu wuta.

A cewarsa, a karshen arangaman, an kashe yan ta’addan Boko Haram biyar yayinda wasun su suka tsere da raunukan harbi.

Ya bayyana cewa dakarun sun kuma kwato wani bindigar Pulenyot Kalashnikova Tankovyy (PKT), bindigogin AK-47 uku, wasu mujallar bindigogin AK-47.

Onyeuko ya kara da cewa an kuma kama tare da lalata wasu kayan hada bama-bamai da sauransu.

Ya ce sabon farmakin da dakarun ke kaiwa sauran yan Boko Haram na nuna kawo karshen duk wasu yan ta’adda a arewa maso gabas.

A cewarsa, dakarun Operation Tura Takaibango sun cancanci jinjina kan jajircewa da kokarinsu na kakkabe sauran yan ta’addan daga mabuyarsu.

“An kuma karfafa masu gwiwar cewa kada su yi kasa a gwiwa illa kara bunkasa nasarar da suka samu.

“Don haka ana ba dukkanin mutanen arewa maso gabas tabbacin sabonta kokarin rundunar (*5*) Najeriya don rugurguza sauran yan Boko Haram daga mabuyarsu a yankin nan,” in ji shi.

A wani labarin, dakarun sojojin Najeriya bakwai ne ‘yan bindiga suka kashe yayin wani arangama da suka yi a hanyar Mararaba-Udege a karamar hukumar Nasarawa ta Jihar Nasarawa kamar yadda Premium Instances ta ruwaito.

Sojojin da ke 177 Guard Battalion na barikin Shitu Alao da ke Keffi a Jihar Nasarawa sun rasu ne sakamakon harin kwantar bauna da ‘yan bindigan suka yi musu.

A cewar majiya kwakwara wanda bai so a ambaci sunansa saboda dalilan tsaro, sojojin da suka mutu suna cikin tawagar sojoji 13 ne da Kyaftin Felix Kura ya yi wa jagora zuwa dajin.

What's On Your Mind?