Daga Ranar Litinin 28 Ga Watan Ramadan Zuwa 1 Ga Watan Shawwal 1442

- Advertisement -

Daga Ranar Litinin 28 Ga Watan Ramadan Zuwa 1 Ga Watan Shawwal 1442

LITININ

Yau Litinin, ashirin ta takwas ga watan Ramadan, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da goma ga waran Mayu, shekarar 2021.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi saraluna da sauran shugabanin al’uma su dinga faɗa wa matasa gaskiya, cewa idan solar lalata ƙasar wa zai gyarata nan gaba?

Fadar Shugaban Ƙasa ta ce Shugaban Ƙasa ya ce ya gode, ‘yan yawon Sallah ko gaisuwar Sallah, kowa ya yi zamansa a inda yake, don kiyayewa da kwaronabairos. Ba sai an je masa ba.

Fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta ba da umarnin a soma duban watan Shawwal daga gobe Talata 29 da goshin almuru. Sai dai ana ta hasashen bana azumi 30 za a yi, da ke nuna ko an nemi jinjirin watan gobe, ba za a gan shi ba, sai jibi Laraba da goshin almuru.

Malamai na ci gaba da tunatar da waɗanda za su fitar da zakkar fid-da-kai, in shinkafa kake ci, to shinkafar za ka fitar ka bayar. In masara kake ci ita za ka bayar. Amma ba masarar mai kwari ko tsutsa ka lalatacciya wato wacce ta lalace ba.

Fadar Sarkin Katsina, da ta Sarkin Daura duk solar ce ba Hawan Daba a wannan Sallar saboda kiyayewa da batun kwarona da sauransu.

A dai Katsinar kuma yankin ƙaramar hukumar Safana, wasu ‘yan bindiga solar kashe mutum eight.

A maƙwabciyar jihar ta Katsina wato jihar Kaduna nan ma kisan aka yi. Wasu makasa suka kashe wani sakatare na mai gari, da matarsa da sirikarsa a yankin ƙaramar hukumar Jema’a. Haka nan a Kachia ta jihar ta Kaduna, wasu fusatattu solar kashe wani mutum da suke zargin ya kashe wani.

A jihar Neja addu’a aka taru aka yi, ta roƙon Allah Ya kawo tsaro a jihar. Sai mutum 28 da suka riga mu gidan gaskiya a jihar a wani haɗarin kwale-kwale.

A jihar Kano sojoji solar kama mutane goma sha uku da suke zargin ‘yan ƙungiyar Boko Haram ne.

Wani mai nazarin al’amuran soja na duniya, ya ce abin da Amurka ke ware wa ɓangaren soja a kullum, shi Nijeriya ke warewa ɓangaren na soja a shekara.

TALATA

Yau Talata, ashirin da tara ga watan Ramadan, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da goma sha ɗaya ga watan Mayu, shekarar 2021.

Bayanai na nuna saura ƙiris wasu fataken dare da suka je Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja tsakanin talatainin dare da goshin asubah, su yi wa babban shugaban ma’aikatan Shugaban Ƙasa Farfesa Ibrahim Gambari sata, sai dai ba su taki sa’a ba kamar yadda bayanan suka nuna.

Gwamnatin Tarayya ta ankarar cewa za fa a ci gaba da kai wa gidajen yari hari.

Gwamnatin Tarayya ta dawo da dokokin kiyayewa da harbuwa ko yaɗa kwaronabairos a ƙasar nan. Daga ɗazu ƙarfe 12 na dare, da suka haɗa da hana duk wani taro ko taruwa da ta haura mutum 50, dole idan za a shiga wurare na gwamnati da sauransu a sa takunkumi, da dole duk wani taro a yi shi ta intanet ko bidiyo ba ga da ga ba, da ci gaba da rufe gidajen cashewa da dabdala da daddare, da doka ta hana walwala, sai dai ba a hana tafiye-tafiye cikin jiha ba.

Kuɗaɗen shiga daga harajin tamanin kaya wato VAT, da gwamnatin tarayya ta samu a watannin uku na farkon shekarar nan, Naira Biliyan 496.39, wato solar haura Naira Biliyan 454.69 da aka samu a watani huɗu na ƙarshen shekarar da ta gabata da ke nuna yawan kuɗin ya ƙaru da kashi 9.17 cikin ɗari.

Gwamnatin Tarayya ta ba da gobe Laraba, da jibi Alhamis a matsayin hutu don gudanar da shagulgulan Sallah, a koma aiki Juma’a.

Daga ranar Lahadi, 16 ga watan nan, ƙungiyar ƙwadago za ta dakatar da komai a jihar Kaduna, su tsaya cik waje guda ba motsawa, don nuna rashin amincewa da korar ma’aikata da sauransu da gwamna El-Rufai ya yi.

Jiya da goshin asubah kidinafas suka je masallaci da ake tahajjud a Jibiya ta jihar Katsina, suka jidi masallata 40, 28 suka suɓuce musu, saura masallata 12 a hannunsu.

Ƙungiyar Yarbawa musamman da ke Legas, ta gargaɗi kungiyar Inyamurai da ke son ta ɓalle har take ta lalata dukiyoyi, cewa hawainiyarta ta kiyayi ramar Legas da sauran garuruwa na Yarbawa.

Rundunar tsaro a jihohin Yarbawa ta Amotekun, ta kama kidinafas su four, ta ceto mutum uku daga hannunsu a Akure ta jihar Ondo.

LARABA

Yau Laraba, talatin ga watan Ramadan, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da goma sha biyu ga watan Mayu, shekarar 2021.

Ta tabbata azumin bana talatin za a yi. Masu hasashe solar ce azumin baɗi ma mai talatin ne. Saboda haka gobe Alhamis Sallah, amma hutun da gwamnati ta bayar, ya soma daga yau jajibari, ya ƙare gobe Alhamis, jibi Juma’a a koma aiki. Abin da ke da wuyar gaske musamman ga ma’aikata da ke aiki a wasu garuruwa. Misali kana zaune a Kaduna, kana aiki a Abuja. Ka ga zai yi wahala ka koma aiki Juma’a, alhali Asabar, da Lahadi ba aiki.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya umarci jami’an tsaro cewa lallai yana so ko ana ha maza ana ha mata, ya ji solar magance matsalar tsaro da ke ci gaba da ta’azzara a yankin Kudu Maso Gabashin Ƙasar nan, da Kudu Maso Kuɗancin Ƙasar nan.

‘Yan sanda solar daƙile wani hari da ‘yan ƙungiyar Boko Haram suka yunƙura don kaiwa Maiduguri ta jihar Barno jiya da yamma. ‘Yan sandan solar kashe eight daga cikinsu.

Kidinafas da suka yi kidinafin ɗaliban jami’ar Greenfield da ke jihar Kaduna, solar yi ragi a ƙudin da suka yi wa ɗaliban.

A jihar Sakkwato wasu ‘yan bindiga solar yi wa motar ‘yan sanda da ke sintiri kwanton-ɓauna, suka kashe ɗan sanda ɗaya.

Gwamnonin jihohin kudu solar hana kiwon sake wato Open Grazing, da hana tafiya da dabbobi daga Arewa zuwa Kudu da kafa, da buƙatar Shugaban Ƙasa ya yi wa al’umar ƙasar nan jawabi a kan matsalar tsaro da ake ciki.

Ƙungiyar Dattawan Arewa ta buƙaci a binciki wani jirgi mai saukar ungulu da aka ce an kama.

Garba Shehu, ya sa a dandalinsa na Twita cewa su Da’u fataken dare solar leƙa fadar shugaban ƙasa, amma sasan Farfesa Gambari, kodayake solar shiga ba sa’a don ba su iya ɗaukar komai ba, can kuma ko me ya faru, sai aka ga Garba Shehun ya goge labarin daga dandalin nasa.

Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta aike wa ‘ya’yan ƙungiyar tunatarwar su jefa ɗayanin jihar Kaduna a duhu dinɗim in an soma yajin aikin da aka tsara yi, na tsayar da komai cik a jihar Kaduna, don nuna wa gwamna El-Rufai ba a yarda da korar ma’aikata da ya yi a jihar Kaduna ba

A jihar ta Kaduna ana nan ana ci gaba da rusau da talatainin dare, na musamman wuraren kasuwanci.

ALHAMIS

Yau ɗaya ga watan Shawwal, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S. A. W. Daidai da goma sha uku ga watan Mayu, na shekarar 2021.

Yau take Sallah Ƙarama/ƙaramar Sallah wato Idil-Fitir, da ke nuna an kawo karshen azumin watan Ramadan na bana, da aka yi talatin. Kodayake wasu jiya suka hau Idi, bayan solar yi azumi 29, da bayayin solar ga wata, ko kuma solar ji an ga wata. Ana buƙatar a fitar da zakkar fid-da-kai kafin a tafi Sallar Idi, a kuma ci wani abu kafin a tafi, hanyar da za a bi zuwa Idi, in za a dawo a sauya/canza wata, ana tafiya ana karbarbari. In an idar da Sallah ana tsayawa sauraron huɗuba, da za ta mayar da hankali a kan halin da ake ciki, da kuma roƙon Allah.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya nemi a haɗa kai, musulmi da kirista, a wannan lokaci na Sallah, don roƙon Allah Ya mana maganin abubuwan da ke damun ƙasar nan.

Gwamnatin Tarayya ta miƙe tsaye, wajen ganin ta sanya ido ga waɗanda ke zuwa ƙasar nan daga Indiya, da Burazil da Turkiyya, da sabon nau’in ciwon kwaronabairos ya yi wa ɓarna ba ƙadan ba, don hana su kawo ta Nijeriya, kodayake an ce an gano wasu da cutar a can jihohin kudu biyu. Gwamnati ta dawo da matakan kariya da rigakafi, har da masallatan da za a hau Sallar Idi yau.

Shugaban Hukumar EFCC Bawa, ya ce solar ƙwato dala miliyan 150, da gidaje 80 daga hannun Diezani.

A watanni uku na farkon shekarar nan, Gwamnati ta samu Naira Biliyan ɗari huɗu ba wasu ‘yan canji daga harajin kamfanoni.

Muƙaddashin shugaban ‘yan sandan Nijeriya, ya ƙarfafa tsaro a ko’ina don tabbatar da an gudanar da bukukuwan Sallah lami lafiya.

‘Yan Majalisar Dattawa da na Majalisar Wakilai da suka fito daga kuɗancin ƙasar nan, solar goyi bayan abubuwan da gwamnonin kuɗancin suka cimmawa a taronsu a kan ƙasar nan ciki har da batun hana kiwon sake.

Ƙungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i, da ta ma’aikatan lantarki, da ta ma’aikatan mai da sauransu, na ta ba da umarni ga ‘ya’yan ƙungiyoyin, da ke jihar Kaduna, su tsayar da komai cik a jihar, daga ranar Lahadi mai zuwa, 16 ga watan nan, don nuna ɓacin a kan korar ma’aikata su fiye da dubu huɗu da gwamnan jihar Kaduna El-Rufai ya yi. Za a tsayar da komai ya tsaya cik na tsawon kwana biyar a matsayin gargaɗi ga gwamnan.

- Advertisement -