Da Gaske Matasan Hausawa Mayunwata Ne?

- Advertisement -

Da Gaske Matasan Hausawa Mayunwata Ne?

Daga: Yaseer Kallah

Tun haduwarmu a sansanin bautar kasa na jihar Gombe muka saba da Jessica. ‘Yar kabilar Igbo ce daga Jihar Imo. Mun yi mutunci sosai da ita da har ta kai bayan mun kammala bautar kasar ba mu yanke zumunci da martaba juna ba.

Muna daukar lokaci mai tsawo muna tattaunawa ta shafukan sada zumunta,
musamman Whatsaap da Fb.

Jessica na da mutunci matuka amma abu daya ne yake hada ni rigima da ita. Ba kuma komai ba ne face kabilanci da jin harshensu da al’adarsu na gaba da na sauran ‘yan Nijeriya.

Na taba rubuta rubutacciyar waka ta Turanci (Poem) mai taken
(Ignore The Rock Oil) ma’ana mu yi watsi da man fetur. A cikin wakar nake nuna tarin albarkatun da Allah ya hore mana a yankin Arewa da bai dace mu wani damu da man fetur din da kullum ake mana gori a kai ba. Nake nuna cewar gara mu rungumi tarin arzikin da Allah ya hore mana wanda in muka alkinta shi za mu iya samun arzikin da ya fi na man fetur.

Ban san ya aka yi Jessica ta ci karo da wakar nan ba wadda na jima da daura ta a kan bangon Fb dina. Ashe da ta karanta abin ya dan sosa mata rai da har ta ji ba za ta iya jurewa ba. Hakan ya sa ta biyo ni har Whatsaap domin maida min da martani.

Bayan mun dan taba hira na dan lokuta sai cikin hikima ta dan soko min magana a kan wakar. Ta fara da ce min na ga wakar da ka yi a kan amfanin rike noma tare da watsi da man fetur.

Sai na amsa mata da cewar “e ai ma tsohuwar waka ce”. Zato nake yi wai yaba min za ta yi, ashe ita wai martani za ta maida min. Budar bakinta ke da wuya sai cewa ta yi, “Ku dai Hausawa kullum sai kurin kuna da kasa mai kyau da take fitar da hatsi mai tarin yawa da kuma yanayi mai kyau wanda ke
taimaka maku gurin kiwo. Kuna mana surutun ba ku da kudan tsando da matsalar malalar mai a cikin ruwa, amma duk da hakan kun fi kowa nuna yunwa a kasar nan.”
Abun ya daure min kai tare da tunzura ni amma na hadiye fushin domin jin hujjarta. Tunanina zan ji ta kafa min wasu kwararan hujjoji amma sai na ji ta ce, “Duk ‘yan Nijeriya ban ga matasan da ke yada hotunansu suna cin abinci a shafukan sada zumunta kamar matasan Hausawa ba. Ka je Fb, Instagram ko Twitter ka gani. Yaron Bahaushe ne da ya tsinci kanshi a dakin sayar da abinci (restaurant) zai fara daukar
hotonsa rike da farantin abinci yana daurawa a shafukan sada zumunta. Za ka ga wani sai ya sa cokali ya debo loma ya dangana a bakinsa sannan zai dau hoton. Wani kuma sai ya riko cinyar kaza ya kai kusa da bakinsa sannan zai dauka ya maka a shafin sada zumunta. Shi dai wai a gan shi yana cin
kaza. Wasu kuma yaran Hausawan a gidansu ne ma za a dan canja miya, sai ka ga wai dole sai ya dau hoton ya yada a duniya wai a ga abin da zai ci. Wani ma duk abin da aka dafa a gidansu sai ya nuna wa duniya. Mu a gurinmu hakan tsabagen nuna yunwa ne da rashin koshi.

Abin da yake kara ba
ni mamaki shi ne, a lokacin da babu abun da muka sa gaba a kan kafafen sada zamunta sama da tattaunawa a kan ci gaban yankinmu da kokarin yadda za a bamu kasarmu ta Biafra, su
‘ya’yan Hausawa burinsu su dauki hoto a dakin cin abinci ko kuma rike da farantin abinci. Abun da na sani shi ne, a duk lokacin da ka dauki hotonka rike da wani abu sannan ka daura
a kan shafukan sada zumunta, kana nuna wa duniya cewar wannan wani abu ne mai matukar mahimmanci da ba ka saba rikewa ba. Yanzu kuma da Allah ya sa ka samu, to bari ka nuna wa duniya domin a taya ka murnar samun sa. Saboda haka ni ba zan taba yarda da babu abun da ya damu yaran Hausawa sama da abinci ba sai na ga solar dena tallar kansu rike da shi.

Ba zan yarda solar koshi ba sai na ga solar rungumi wani abu daban. Idan kuma kana ganin na gaya maka hakan ne don in muzanta kabilarku, to don Allah ka koma kan shafukan sada zumunta kai ta dubawa. Ba makawa za ka ga wancan rike da cinyar kaza; wancan rike da lemo, waccan ta sa faranti a gaba
wai a ga me za ta ci a gidansu; wancan ya sa nama a baki; wadancan wai taro suke yi amma so suke a ga farantai a
gabansu da sauransu.” Na dan yi shiru na rasa me zan ce. Ni dai na san mu ba mayunwata ba ne, amma kuma ban san ya zan kare kanmu ba.

Amma kuma da na koma shafukan sada zumuntar sai na ga kuma fa ga ire-iren hotunan da ta kafa hujjar da su ringis.

- Advertisement -