Da duminsa: Bayan sa’o’i kadan da zuwan ministan tsaro, Boko Haram sun kai farmaki Borno

0
162

Da duminsa: Bayan sa'o'i kadan da zuwan ministan tsaro, Boko Haram sun kai farmaki Borno

Kasa da sa’o’i hudu bayan ziyarar da minsitan tsaro, Bashir Magashi tare da hafsoshin tsaro zuwa Maiduguri, mayakan Boko Haram sun kai farmaki karamar hukumar Dikwa dake jihar Borno a ranar Lahadi.

Dikwa tana yankin tsakiyar jihar Borno ne kuma tana da nisan kilomita 85 zuwa babban birnin jihar na Maiduguri, Vanguard ta ruwaito.

Bayanan da aka samu daga majiyoyi sun tabbatar da cewa, mayakan ta’addancin dauke da makamai da motocin yaki a halin yanzu suna musayar wuta da jami’an tsaro domin su samu kutsawa garin.

Suna son shiga domin tada zaune tsaye. Karar harbe-harbe ta fashe-fashe ya gwauraye yankin wurin karfe 7 na ranar Lahadi.

An Kaiwa Gwamna Zulum Hari A Karo Na Uku

Dikwa tana fuskantar jerin miyagun hare-hare daga mayakan ta’addanci a cikin kwanakin nan.

Karin bayani na nan tafe…

A wani labari na daban, hukumar yaki da fasa-kwabrin miyagun kwayoyi (NDLEA) ta cafke wasu ‘yan kasar Chadi da Nijar dake samarwa miyagun ‘yan ta’adda kwayoyi a Najeriya.

An cafkesu ne a makon da ya gabata a jihohin Taraba da kuma Nijar, Day by day Belief ta ruwaito.

Shugaban hukumar NDLEA, Buba Marwa, ya bayyana hakan a Abuja yayin da shi tare da kungiyarsa suka ziyarci ministan yada labarai da al’adu na kasar nan, Lai Mohammed.

What's On Your Mind?