Da Dumen Sa: Yan Bindiga Sun Nemi Kudin Fansa Miliyan 270 Akan Ɗalibai

0
151


Labarin Masu garkuwa da mutane solar sa kudin fansa a kan ɗaliban jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, da aka sace a kan hanyar zuwa birnin tarayya Abuja a makon da ya gabata.

‘Yan Bindigar solar nemi a biya Naira miliyan 270 kafin su fito da wadannan ɗalibai har tara da su ka tsare, ko kuma labari ya sauya.

Wani daga cikin wadanda ‘yan bindigan su ka tsare, Dickson Oko, ya yi nasarar kubuta, ya kuma shaida wa manema labarai halin da ake ciki.

Dickson Oko ya ce miyagun solar tuntubi ‘yanuwan ɗaliban da su ka tsare inda su ka bukaci kowanensu ya biya miliyan 30 a matsayin fansa.

Oko wanda ya aka yi wa rauni da bindiga a dalilin harin ya na samun sauki a yanzu, amma hankalinsa a tashe ya ke saboda tsare takwarorinsa.

Matashin ya shaida wa manema labarai cewa ya na cikin wadanda su ka tsere a lokacin da ‘yan bindigan su ka tare su a kan hanyar su ta zuwa garin Abuja. Mista Oko ya ce shi da direbansu mai suna Nuruddeen Mohammed solar ci kafar kare, inda har ya bar wayoyin salularsa da wasu kaya a cikin motarsu.

Mutane 12 ne a wannan mota da ta dauko yaran makarantar, daga ciki an kama mutum tara. Iyalan wata mace daga cikin ‘daliban solar fada wa VOA Hausa cewa masu garkuwa da mutanen solar tuntube su, kuma solar bukaci miliyan 30 daga gare su.

What's On Your Mind?