Da Dumen Sa: Mai Jaridar Leadership Ya Rasu

0
69


Buhari Ya Ce An Yi Babban Rashi A Fagen Aikin Jarida, Allah Ya Yi Wa Shugaba Kuma Mawallafin Jaridun Leadership, Mista Sam Nda-isaiah, Rasuwa A Daren Jiya Juma’a, 11 Ga Disamba, 2020, Ya Rasu Ya Na Da Shekara 58 A Duniya.

Mista Nda-isaiah Ya Rasu Ne Bayan Rashin Lafiya Na Kwana Ɗaya Kacal.

Wata Ƙwaƙƙwarar Majiya Ta Faɗa Wa Mujallar Fim Cewa Har Ma Ya Je Aiki A Ofishin Sa A Ranar Alhamis, Inda Ya Yi Mitin Da Wasu Jagororin Kamfanin Recreation Da Wata Sabuwar Jarida Da Ya Kafa.

Majiyar Ta Ce Amma Ya Bayyana A Wajen Taron Cewa Ba Ya Jin Daɗin Jikin Sa. “Da Zai Tafi Gida Ma Sai Da Aka Kama Masa Kafaɗun Sa, Aka Riƙe Shi Har Zuwa Jikin Motar Sa, Ya Shiga, Direba Ya Tafi Da Shi Gida,” Inji Majiyar.

Jiya Kuma Aka Kai Shi Babban Asibitin Maitama, Abuja, Inda Da Dare Ya Cika.M, Labarin Mutuwar Sa Ya Girgiza Mutane Matuƙa.

Nda-isaiah Dai Ya Karanci Ilimin Haɗa Magunguna Ne (Pharmacy) A Jami’ar Obafemi Awolowo Da Ke Ile-ife. Ya Fara Aiki A Babban Kamfanin Nan Na Magunguna Mai Suna Pfizer, Kafin Ya Bari Ya Shiga Harkar Kasuwanci.

Ya Kafa Jaridar Leadership Ne A Cikin 2004 Bayan Ya Shafe Shekaru Ya Na Rubuta Wani Filin Sharhi A Cikin Jaridar Day by day Belief, Inda A Nan Ne Ya Fara Yin Suna.

Leadership Ta Fara Fita Ne Mako-mako Kafin Ta Zama Mai Fitowa Kullum-kullum A Cikin Janairu, 2006.

A Cikin 2006 Ɗin Kuma Ya Fito Da Jaridar Hausa Ta Mako-mako Mai Suna Leadership Hausa, Wadda Bayan Shekaru Ya Maida Ita Jarida Mai Fitowa Kullu-kullum Tare Da Sabon Suna Na Leadership A Yau.

Mujallar Fim Ta Yi La’akari Da Cewa Nda-isaiah Mutum Ne Mara Tsoro A Rubutun Sa, Kuma Mawallafi Ne Wanda Ke Da Ƙoƙarin Fito Da Sababbin Hanyoyi Na Bunƙasa Kasuwancin Sa, Wanda Hakan Ya Sa Kamfanin Leadership Ya Yi Matuƙar Bunƙasa Har Ya Zamana Ɗaya Daga Cikin Manyan Kamfanonin Jarida A Nijeriya.

Kamfanin Ya Mallaki Jaridu Daban-daban, Kuma Ya Na Kan Hanyar Mallakar Gidan Rediyo Da Talbijin.

Wata Majiya Ta Faɗa Wa Mujallar Fim Cewa Kamfanin Ya Shiga Matsalolin Rashin Kuɗi Da Kuma Gudanarwa A Cikin ‘yan Shekarun Nan, To Amma Mawallafin Ya Fara Yin Garambawul Ɗin Da Ya Soma Saita Shi Ta Yadda Har Ya Koma Ya Na Biyan Albashi A Kan Kari.

Nda-isaiah Dai Ya Karanci Ilimin Haɗa Magunguna Ne (Pharmacy) A Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. Ya Fara Aiki A Babban Kamfanin Nan Na Magunguna Mai Suna Pfizer, Kafin Ya Bari Ya Shiga Harkar Kasuwanci.

Ya Shiga Fagen Aikin Jarida Ne Lokacin Da Ya Kafa Wata Ƙasida Ko Mujalla Mai Fitowa Wata-wata Mai Suna Leadership Confidential, Wadda Ita Ce Ta Rikiɗe Ta Zama Jaridar Leadership.

A Cikin 2003 Ya Zama Daraktan Yaɗa Labarai Na Rundunar Takarar Shugaban Ƙasa Ta Janar Muhammadu Buhari (Ritaya). Bayan An Faɗi Zaɓe Ne Ya Kama Jaridar Tasa.

Nda-isaiah Ya Shiga Takarar Zama Shugaban Ƙasa Da Aka Yi A 2019 A Ƙarƙashin Tutar Jam’iyyar Apc, Inda Maigidan Sa, Muhammadu Buhari, Ya Kada Su A Zaɓen Share Fage Da Aka Yi A Legas.

A Saƙon Ta’aziyya Da Shugaban Ƙasa Buhari Ya Bayar A Yau, Ya Bayyana Alhini Da Baƙin Ciki Kan Wannan Babban Rashi, Ya Kira Nda-isaiah Da “aboki Na Ne Kuma Abokin Hulɗa Ta”.

Shugaban Ya Yi Wa Iyalin Mamacin Da Kuma Dukkan Masu Aikin Yaɗa Labarai Da Abokai Da ‘yan’uwa Gaisuwa, Ya Ce, “ƙasar Nan Ta Yi Rashin Mutum Mai Aƙida, Wanda Ya Kafe Tare Da Jajircewa Kan Abin Da Ya Yi Amanna Da Shi Na Gyaran Nijeriya.

“za A Daɗe Ana Jin Raɗaɗin Rashin Sa. Wannan Babban Kifi Ne Wanda Ya Fice Daga Tekun Aikin Jarida.”

A Makon Jiya Ne Aka Zaɓi Nda-isaiah A Matsayin Ɗaya Daga Cikin Dattijan Ƙungiyar Mamallaka Gidajen Jaridu Ta Nijeriya, Wato ‘newspaper Proprietors Affiliation Of Nigeria’ (Npan).

Ɗan Asalin Jihar Neja, An Haifi Sam Nda-isaiah Ne A Ranar Ga Mayu 1, 1962 A Minna. Mahaifin Sa Ya Na Daga Cikin Manyan Editocin Jaridar New Nigerian, Kuma Sam Ya Sha Faɗin Cewar Wannan Ne Ya Saka Masa Son Aikin Jarida A Zuciyar Sa.

Nda-isaiah Dai Ya Rasu Ya Bar Matar Sa, Zainab (Wadda ‘ya Ce Ga Birgewa Mamman Remawa) Da Kuma ‘ya’yan Su.

Mite Fatanku Zuwa Gareshi?? feedback And Share.

What's On Your Mind?