Da Dimi-diminsa: ‘Yan Boko Haram Ba Su Shigo Bauchi Ba, Inji ‘Yan Sanda

0
172

Da Dimi-diminsa: ‘Yan Boko Haram Ba Su Shigo Bauchi Ba, Inji ‘Yan Sanda

Daga Khalid Idris Doya,

Rundunar ‘yan sandan Jihar Bauchi ta sanya kafa ta shure rahotonnin da wasu kafafen yada labarai suka yada da ke cewa wasu ‘yan Boko Haram ko ‘yan ta’adda solar kwararo zuwa cikin Jihar Bauchi.

Rahotonnin da aka yada da ke cewa ‘yan ta’addan da ake kyautata zaton ‘yan Boko Haram ne solar shigo Bauchi ne ta karamar hukumar Gaidam, sai dai ‘yan sandan solar ce sam ba haka zancen yake ba.

A sanarwar manema labarai da Kakakin ‘yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Waki, ya fitar cikin daren nan, ya bayyana cewar labaran da kafafen yada labarai suka yada, solar jingina da cewa solar samu bayanin ne daga bakin sakataren gwamnatin jihar Bauchi, Sabiu Baba wanda ya bayyana musu bayan wani taron zama na gaggawa kan tsaro da masu ruwa da saki suka yi karkashin jagorancin Gwamna Bala Muhammad a a gidan gwamnati ranar Litinin.

Wakil, ya ce zaman da masu ruwa da tsaki suka yi kan tsaro, an yi ne bisa rahotonnin shigowar wasu mazauna Gaidam da Kanam da suke jihar Yobe bayan harin da ‘yan Hoko Haram suka kai yankunan.

“A ganawar manema Labarai, SSG ya bayyana cewar an tattauna domin ganin an dauki matakan da suka dace tare da samar da wadaccen tsaro domin kare jihar daga abubuwan da suke faruwa a jihohin makwabta.

“Har ya kafa hujja da wasu da suka shigo jihar da har suka sace kayan kamfanin sadarwa na MTN kuma tunin aka kama biyar daga cikinsu.”

A don haka ‘yan sandan suka ce babu wani dan Boko Haram da ya shigo Bauchi, “Muna kira ga jama’a da su yi watsi da labaran da ke cewa ‘yan Boko Haram solar shigo Jihar Bauchi, sannan su cigaba da tafiyar da harkokin rayuwarsu na yau da gobe.”

Daga nan dai ‘yan sandan solar nemi jama’a da suke kai musu rahoton dukkanin wani motsin da suka gani domin daukan matakan da suka dace.

 

Cikakken labarin na tafe.

What's On Your Mind?