Da Bashi Mu Ke Biyan Kudin Fansa, Cewar Alummar Jihar Neja

- Advertisement -

Da Bashi Mu Ke Biyan Kudin Fansa, Cewar Alummar Jihar Neja

Daga Maigari Abdulrahman

Jihar Neja na fama da karin yawaitar hare-haren ýan bindiga a ýan kwanakin nan tamkar ruwan dare.

Garuruwa da dama ne maharan su ka afkawa tarae da tayar da wasu daga ciki, ga kuma garkuwa da mutane inda su ke karbar kudin fansa bayan azabtarwa. Jamián tsaro kuma kamar dai lamarin ya soma fin karfinsu. Wakilinmu, Justina Asishana ya ziyarce kananan hukumomin da lamarin ya addaba, ga kuma rahoton da ya hada na halin kuncin mazauna yankunan.

Asabe Mathew na dai daga cikin ýan gudun hujira a wata firamarin da ke karamar Hukumar Munya ta Jihar Neja din,rayuwa ta zamo mata wani abu daban yanzu, yaranta biyu a ka yi garkuwa da su, wanda hakan ya tilasta ta sayar da dukkan wani abu da ta mallaka domin biyan kudin fansa.

“Solar kassara rayuwata. Na sayar da dukkan kayan gona na, har ma sai da na ranto bashi domin cika kudin fansan ýayana. Yanzu banda komai a rayuwata,”in ji Asabe tana fadi a cikin kuka.

Da take bada labari, ta ce, “A kan hanyar dawowa makaranta a ka dauke yaro na, wanda su ka yi garkuwar da shi su ka kira suna neman fansar miliyan daya. Bani da zabi illa na nemo kudin na biya, ko kuma su kashe shi. Na sayar da komai, har sai dai na nemo bashi na hada, in ji ta.
“Haka ýa ta ma, ita su ka fara dauka a baya, sai da muka nemi kudin fansa.

Yanzu bani da komai a rayuwata. Alámurra solar yi mana tsauri sosai, rayuwa ta yi kunci sosai.”
Kamar Asabe, shi ma Malam Muhammad Isah yaransa biyu a ka dauke a harin baya da maharab su ka kai. Shima yana sansanin ýan gudun hijira.

Ga abinda Muhammad yake labartawa, “Jiya na gudo zuwa nan bayan harin ýan bindigar, a yayin harin, solar dauke yara na biyu, ba ni da kudin biyan fansar da su ka nema ta miliyoyi,ian zan iya samun su? Ba zan iya komawa kauyenmu ba naked na sayar da kayan gona ta, komawa kauyen kamar ina kai kaina ne ga mutuwa,” in ji shi.

Gama-gari, shi ma mataimakin shugaban karamar hukuma, Luka Garba bai tsira ba, inda maharan su ka kashe kanen sa a watanni baya. kanen nasa, yana dai daga cikin ýan sa kai na garin Kachu, kamar yadda ya shaidar.

Yawaitar rashin tsaro a karamar Hukumar Munya
Munya karamar hukuma ce a cikin Jihar Neja, ta hada iyaka da Jihar Kaduna. Dayawan mazauna garin na zargin hada iyaka d aKadunar a matsayin dalilin yawaitar matsalar tsaron da ke addabar karamar hukumar.

Hare-haren ýan bindiga ya soma ne a yankin kimamin shekaru shida, kuma abin sai dada kamari yake, dalilin hakan yankin ya zama abin tsoro da kowa ke gudu. Mahara kan kai hari kowane lokci, su sace mutane su yi duk abinda su ka ga dama.

Saboda matsalar tsaron, ya sa mazauna ba sa iya fita gona ko sauran harkokin kasuwanci, wanda hakan ya illata harkar tattalin arzikin yankin. Ýan kasuwa solar daina fita dauko kaya, wanda hakan hanyar ya rage shigar haraji.

Ba farar hula ba, har jamián tsaro maharan na farmaka, ranar 21 ga Aprilun 2021, maharan solar farmaki sansanin soja a Allawa, karamar Hukumar Shiroro, inda su ka kashe soja biyar tare da dan sanda, tare da kona sansanin kafin daga bisani su shiga kauyen su kashe mazauna bakwai.

Akwai karancin rahoton Hare-haren da ke faruwa a karamar Hukumar Munya, an fi bada karfi ga na karama Hukumar Shiroro, ba mamaki saboda sansanin kamfanin lantarki da ke nan ne yasa ake basu kulawa fiye da Munya.

A yayin wata ziyara. Wakilinmu ya ci karo da wasu mata suna gudun ceton rai bayan bullar ýan bindiga a yayin da su ke noma a gona, kamar yadda dai daga cikinsu ta shaida.

“Muna cikin aiki gona muka hangi zuwan su. Ba abinda za mu yi face guduwa. Gashi mun cire anfanin gona, amman ba yanda za mu yi mu dauka dole mu yi ta ranmu,”in ji Louis dai daga cikin matan.
Haka rayuwa ta koma yanzu a Munya, ba kwanciyar hankali ba kuma nastuwar zuwa gona, duk da cewar mafiya yawan mazauna garin manoma ne, amman noman ya gagara yanzu, kamar yadda wasu mazauna suka shaida.

Wani shugaban kungiyar matasa, wanda ya nemi a sakaya sunan sa, ya ce maharann da sabbin mashuna su ke anfani wurin kai hari, wanda hakan ke basu damar mamayar mutane cikin sauri kafin su ankare.

Mista Luka Graba, mataimakin shugaban karamnar Hukumar Munya, ya ce jamaár garin na yin hijira zuwa Sarkin Pawa, Gwada, Kuta ko da kuma Minna babban birnin jihar, inda ya ce mako biyu d asu kawuce, maharan solar kai farmaki a karamar Hukumar Kuchi, inda su ka kashe ýan sanda uku, dayan yanko rago su masa, in ji shi.

Wannan ne dalilin da ya sa jamián tsaro barin karamar Hukumar Kuchi zuwa Sarkin Pawa. Kwanaki kadan ma, solar kashe wani mai suna Jacob a Zazzagi, solar kuma kai hari sansanin soja inda su ka kona motocin soja da kayayyaki, in ji mataimakin shugaban karamar Hukumar.
Shin Gwamnati ta damu da halin da muke ciki?
Tambayar da mazauna yankin karamar Hukumar Munya ke yi koyaushe shi ne, shin ko gwamnati ta san halin da su ke ciki, ko ko dai solar sani amman ba su damu ba ganin rashin takamaimen yunkurin kare rayuwarsu da dukiyoyinsu.
Mataimakin Shugaban karamar Hukumar ya ce, gwamnati ba ta yin wani abu akai duk da yawan korafin da su ke kaiwa, ya ce matsalar tsaron ta fi karfinsu.

“Shin me gwamnati ke nufi? Mu ba mu gane me hakan ke nufi ba, ko ko dai ba gwamnati ne? Muna iya kokarinmu a matsayinmu na karamar Hukuma. A matsayinana na mataimakin shugaba, tare da mutane na nake kwana domin nasan halin da su ke ciki. Abin ya fi karfinmu, akwai bukatar gwamnatin jiha da ta tarayya su sa hannu.” in ji shi.

Ÿa ci gaba da cewa, “wata tambayar da muke yi kuma ita ce, shin ta ina su ke samun makamai? Ina su ke samun bindigogi? Shin gwamnati ba ta iya kwace makaman, ta ba jamián tsaro su?“
Ita ma Asabe, cewa ta yi, alúmma ba su ga anfanin gwamnati ba a kan rashin tsaron da ya ke addabarsu, tamakr ma gwamnait ta manta da su.

“Ya kamata gwamnati ta kawo mana dauki, muna wahala matuka. Mai yake hana su taimakon mu ne? Idan ýan bimdiga su ka karar da mu, to wa za su mulka kuma? Shin ba mu muka zabe su ba, mai yasa su ka barmu cikin wannna halin?, in ji Asabe
“Mutane solar daina zuwa kasuwanci saboda matsalar tsaro, gwamnati t abarmu cikin halin kunci, ko mu ba mutane ba ne?
Biyan kudin fansa na kara talauta mu, cewar mazauna
Dayawan alúmmar karamar Hukumar Munya na kara samun tsananin tattalin arziki, sakamakon biyan kudin fansa wanda hakan ke tilasta su sayar da kayan gona da sauran kadarori don fanar ýan uwansu.

Garkuwa da mutane ya zama ruwan dare a garin, idan da ana sabawa to da solar saba. Yanzu su kan hada tallafin kudi ga wanda aka dauke wani dan uwansa, domin dai abi ya zama tainakon kai.

“Idan an dauke mutum, mu kan hada ma ýan uwansa kudi domin fanso sa, idan ban bada ba, to nima idan aka kama ni ba za su taimaka ba. Dayawan mutane yanzu basada kayan gona saboda biyan kudin fansa,”in ji wani shugaban matasa
Mataimakin shugaba ya bayyana cewar, akwai mata 20 a hannun masu garkuwa da mutane, suna neman miliyan 20 kudin fansa, ya ce suna bakin kokari don ganin an hada kudin domin ceto su.
Matasa ga gwamnati: A bamu makamai, za mu kare kanmu
Matasan yankin solar bayyana shirinsu na tunkarar ýan bindigar idan gwamnati ta samar masu da makamai. Wani matashi ya ce, basu da makaman da za su iya tunkarar ýan bindigar, amman idan aka basu, to za su iya kare kansu.
“Matasanmu na iya tunkarar ýan bindigar nan, amman suna jin tsoro ne saboda rashin makamai. Amman, idan da za a bamu makamai, to da za mu kare kanmu. Ba za mu iya tunkarar us da sanda da adda ba. Tsananin da muke ciki ya yi yawa,”in ji wani matashi.
Shi ma Mista Garba, ya yarda da ba matasan makami, “Ina goyon ba matasa makamai domin kariya. Halin da muke ciki ya yi yawa, kuma mutum ba ya fahimta idan ba nan yake ba.
“Gaskiyar magana idan da muna da makamai, to da mun tunkare su. Amman jamián tsaro ba sa yarda, ba sa son ma suji kana fadar makami a bakinka, idan ko aka similar ka da bindiga ko wani makami, to matsala ce, hakan ya sa su ke kisnamu kamar kwari,”in ji mataimakin shugaban karamar Hukumar.
Harin bai bar wuraren ibada ba
A tsakanin watanni hudu, akalla coci hudu maharan su ka kona. Haduwar musulmi ko kiristoci don yi bauta ya zama abin tsoro saboda tunanin kawo farmakin ýan bindiga. Ranakun coci, Lahadi; su ne ranakun da su ka fi kai farmaki, kamar yadda Mista Garba ya shaidar
karamar Hukumar Munya dai ta shahara wurin noman doya, masara da shinkafa. Kafin hare-haren, ýan bindiga, garin ya kaance mahadan kasuwancin kayan gona sosai, to sai dai, matsalar tasaro ta saka fargaba a zukatan baki zuwa garin.
A baya, tun gabanin cire anfanin gona mutane ke kamawa su saye, amman yanzu lamarin ba haka ne ba. Mutane solar daina zuwa saboda matsalar tsaro, kamar yadda wata mata, Martha Egbe ta fada.
Ita ma Asabe, ta koka da halin,inda ta ce, sakamakon rashin zuwan masu siya, hakan ya tilasta ta daukar kayan zuwa Minna babban birnin Jihar. Zuwa Minnar kuma yana da wahala, wani lokacin direbobi
Muna bukatar komawa gidajenmu, ýan gudun hijira ga Gwamnati
Ýan gudun hijira da ke sansanin Firamari solar koka da rashin abinci, solar kuma nemi gwamnati da ta maida su muhallansu. Haka kuma, solar nemi taimakon gwamnati
Ladi Shehu, manomiya ce tana cikin ýan gudun hijira,”Solar kore mu daga garuwawanmu kuma ba za mu iya komawa ba, komawa tamkar kai kai ne ga mutuwa. Ba ma jin dadin zama a nan, ba abinci mai kyau a nan, ba kuma zai yiyu mu koma gida dauko abincin ba, ga yaranmu suna fama da yunwa.”
Wata kuma cewa ta yi, ba su san me za su yi ba, an kashe mazajensu, an yi garkuwa da ýayansu, kuma gwamnati ba ta kai masu dauki ba.
“Abin takaici ne gwamnati ba ta mana komai ba face wannan muhallin gudun hijira. Za mu so gwamnati ta kawo karshen wannna rikicin domin mu samu damar komawa garuruwanmu, mu ci gaba da rayuwarmu kamar yadda muka saba.
Akwai masu raáyin saka dokar ta baci a jihar domin maganin matsalar rashin tsaron, dan majalisa mai wakiltar yankin da abin ya shafa a Jihar, Madaki Malik na dai daga cikin masu raáyin saka dokar ta ba ci.
Saka dokar ta ba ci, a cewar dan majalisar, zai ba gwamnati damar daukar matakin shawo kan matsalar. Matsalar tsaron ta yi kamari, tana dada yaduwa zuwa sauran kananan Hukumomi, in ji shi.
Ya koka da cewar, dukkan makarantun da ke yankin solar koma sansanin ýan gudun hijira, fargaba da tsoro ya cika zukatan mutane, in ji dan majalisar.
To sai dai, a wani bangaren, wasu na ganin saka dokar ta ba cin ba zai kawo nasarar da ake fata ba. A kwanan baya, gwmanan Katsina, Aminu Bello Masari, ya bayyana cewa, saka dokar ta ba ci ba zai kawo karshen matsalar tsaro ba
A cewar sa, akwai karancin jamián tsoron da za a yi anfani da su wurin dabbaka dokar ta ba ci kamar yadda wasu ke kira.
Matsalar tsaro dai na kara tabarbarewa a fadin kasar, musamman yankin arewa, inda jihohi da dama ke fama da matsalar ýan bindiga, masu garkuwa da kuma Boko Haram.
Abinda alúmma su ke ta fata ko yaushe, shi ne kawo karshen matsalar tsaron. Dayawan mutane dai., na ganin gwamnati ta gaza wurin kare dukiyoyi da rayuwalr alúmma.

 

- Advertisement -