Da ɗimi-ɗiminsa: Mutum 4,120 Suka Samu Gurbin Aiki A NIS Daga 500,000

- Advertisement -

Da ɗimi-ɗiminsa: Mutum 4,120 Suka Samu Gurbin Aiki A NIS Daga 500,000

NIS ta fitar da hadawalin sabbin jami’an da za a ɗauka a shekarar nan ta 2021. Inda mutum four, 120 suka samu damar tsallakawa zuwa matakin ƙarshe na tantancewa.

Shugaban NIS CGI Muhammad Babandede ya bayyana cewa a ranar Litinin za a buɗe shafin da waɗanda suka yi nasara za su duba sunayensu da wuraren da za su yi tantancewar ƙarshe.

Ya bayyana haka ne a jawabin da ya yi wa manema labarai a shalkwatar NIS da ke Abuja yanzu-yanzu.

Za mu kawo muku ƙarin bayani

- Advertisement -