CMG Ya Gudanar Da Bikin Nune-nunen Bidiyo Da Hotuna Na Kasa Da Kasa Karo Na Farko

0
83

CMG Ya Gudanar Da Bikin Nune-nunen Bidiyo Da Hotuna Na Kasa Da Kasa Karo Na Farko

Ranar 20 ga wata, a birnin Ganeva, babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, ya gudanar da bikin nune-nunen bidiyo da hotuna na kasa da kasa karo na farko, domin murnar ranar harshen Sinanci ta MDD ta shekarar 2021.

Tatiana Valovaya, babbar darektar ofishin MDD a Ganeva ta halarci bikin, tare da yin jawabi. Inda ta ce harshen Sinanci, harshe ne da aka fi amfani da shi a duniya. Kuma yana daya daga cikin harsuna mafiya dogon tarihi a duniya. Harshen Sinanci ya bayyana hazakar Sinawa, da al’adunsu.
Jakada Chen Xu, zaunannen wakilin kasar Sin a ofishin MDD da ke Ganeva da sauran hukumomin kasa da kasa a kasar Switzerland, ya yi nuni cikin jawabinsa da cewa, a matsayinsa na daya daga cikin harsunan da ake amfani da su a MDD, harshen Sinanci ya taka muhimmiyar rawa wajen kara azama, kan tuntubar juna da cudanyar juna a tsakanin kasa da kasa. Ya ce yanzu baki masu yawa photo voltaic kara koyon Sinanci, tare da kara sanin al’adun kasar Sin. Duniya za ta kara fahimtar kasar Sin mai dogon tarihi, da aiki tukuru da kirki, wadda ke bude kofa ga kowa, da samun ci gaba ta hanyar yin kirkire-kirkire.
Shi ma Shen Haixiong, shugaban CMG, kuma babban edita na CMG, ya taya wadanda suka samu lambobin yabo, da wadanda suka halarci bikin murna. (Tasallah Yuan)

What's On Your Mind?