Cibiyar Riyadulsalihin Ta Ba Maruyu 2000 Tallafin Abincin Azumi Da Kayan Salla A Funtuwa

0
74

Cibiyar Riyadulsalihin Ta Ba Maruyu 2000 Tallafin Abincin Azumi Da Kayan Salla A Funtuwa

CIbiyar tallafawa Marayu, karkashin Masallacin Riyadulsalihin ta tallafawa Marayu 200 da Abincin Azumi da kayan Sallah a karamar Hukumar Funtua cikin Jihar Katsina.

Shugaban CIbiyar , Màlam Yusif Lawandi Sarkin Kara, ya bayyana cewa, wannan shine karo na shida da CIbiyar ke ba Marayu tallafin abinci Azumi da kayan Sallah,a kowace shekara a karkashin Daliban Masallacin Riyadu Salihin da Bakori Highway Funtua.

Hukuncin wanda maziyyi ko maniyyi ya fito masa alhali ya na azumi daga bakin Aminu Daurawa

Kuma a wannan shekarun Marayu 200, za su amfana da wannan tallafin wanda ya hada Abincin Azumi,Shinkafa da sukari da kayan Sallah ga maza da Mata.

Babban Bako mejawabi, Khalifa Ali Saidu Alti Funtua, ya bayyana mahimanci Ciyarwa mu samman ga maraya a cikin wannnan wata mefalala.

“A cewar sa, Khalifa Ali Saidu, A cikin Alkur’ani mai girma Allah ya yi bayani akan falala na taimakawa Marayu da kuma asara da tabewa ga masu cin hakin su naked da izini ba ko sharadi.

Akan haka ne Khalifa Ali ya yi kira ga kungiyoyin da cibiyoyi da dai dai kun mutane wajan koyi da Riyadu Salihin wajen tallafawa Marayu.

daya daga cikin wadanda suka amfana da tallafin, Zainabu Shuaib ta bayyana godiyar su ga Cibiyar Riyadu Salihin wanda a duk shekara ta ke raba wa Marayu gashi a wannan shekar ina daga cikin wadanda suka amfana da tallafin muna godiya ga wadanda suka sa Cibiyar Riyadu Salihin don tallafawa Marayu da gajiyayu.

What's On Your Mind?