Cibiyar Mu’assatul Abdulwahab Ta Tallafa Wa Marayu 115 A Zariya

- Advertisement -

Cibiyar Mu’assatul Abdulwahab Ta Tallafa Wa Marayu 115 A Zariya

Daga Isa Abdullahi Gidan ‘Bakko, Zariya

A farkon wannan makon ne gidauniyar tallafa wa al’umma marasa karfi da kuma marayu, wadda ake kira da sunan Mu’assatul Abdulwahab Islamic Centre wadda ke Unguwar Tudun Jukun a karamar hukumar Zariya a jihar Kaduna, ta tallafa wa marayu maza da mata su 155 da kayayyan abinci.

Taron rabon kayayyakin da kuma tufafin ya gudana ne a bisa shugabancin babban daraktan gidauniyar Alhaji Bala Alba – Bello a babban masallacin da ya gina.

A jawabinsa wajen rabon kayayyakin da aka aambata, Alhaji Bala Alba – Bello, ya farad a cewar, wannan taron bas hello ne na farko ba, domin kamar yadda y ace an shafe shekaru da dama wajen aiwatar da wannan tallafi ga marayu da kuma al’umma maza da mata, wanda a wannan shekara an tallafa wa al’ummomin da aka ambata inda maza marayu 55 da kuma mata 60 suka sami tallafin da aka bayyana.Alhaji Alba- Bello ya yi kira ga al’umma da su rika tallafa wa marayu da kayayyakin abinci da tufafi domin su sami damar das u ma za su gudanar da rayuwarsu, kamar yadda sauran al’umma ke yi, ba lallai sai lokacin azumi ko kuma lokutan sallah ba, a cewarsa, tallafa wa maraya, a kwai ;ada mai yawan gaske daga mai kowa mai komi, wanda mutum zai fara ganin sakamako tun a nan duniya kafin gobe.

Da kuma ya juya ga mawadata, sai ya sake kira garesu na su rika wani bangare na dukiyansu, domin tallafa wa marayu da sauran al’umma da suke bukatar tallafin abin da za su ci tare da iyalansu, duk mai yin wannan, kamar yadda Alhaji Alba – Bello ya nanata, zai ci gaba da ganin haske a rayuwarsa, baya ga fadadan dukiyarsa da zai gani a dan kankanin lokaci.

Sauran wadanda suka yi jawabin a wajen rabon kayayyakin solar hada da Dokta Shehu Umar daya daga cikin ma su wukar yankar magana a gidauniyar da kuma babban limamin masallacin Juma’a na Alba – Bello, Dokta Hamza Al- Sudani da sauran malamai ma su yawan gaske.

A dai lokcin wannan taro, an rarraba tufafi da suka hada da Atamfa da takalma da sada kayayyakin binci da suka hada da dai sauransu.

- Advertisement -