Ci Gaba Da kone Mana Ofisoshi Zai Nakasa Zaben 2023 – INEC

- Advertisement -

Ci Gaba Da kone Mana Ofisoshi Zai Nakasa Zaben 2023 – INEC

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta na kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa, ci gaba da farmakin ofishoshin hukumar a da ke fadin kasar nan zai iya dagula harkokin babban zabe mai zuwa.

Shugaban hukumar ya bayyana hakan ne a ranar Laraba wajen taron gaggawan da hukumar ta kira na kwamishinonin zabe da ke fadin kasar nan wanda ya gudana a Abuja.

Ya ce, “babu ko shakka wadannan farmaki da ake kai wa ofishoshin hukumar INEC za su iya hargitsa shirye-shirye zabe na shekarar 2023.

“A bayyana yake wadannan mummunan ta’addanci da ake yi wa ofishoshin hukumar, ana yin su ne da gangan domin a hargitsa shirin zabe da kuma hanyoyin gudanar da sahihin zabe,” in ji shi.

Hukumar ta gudanar da taron ne a dai-dai lokacinm da wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka cinna wa ofisoshi biyu na hukumar zabe mai zaman kanta wuta a jihar Ebonyi. Ofisoshin suna cikin kananan hukumomin Ebonyi da Ezza ta Arewa a jihar. An bayyana cewa ba a samu asarar rai ko jikkata ba amma akwai barna mai yawa ga ginin da kuma kayayyakin.

Sai dai har yanzu hukumar ba ta fitar da cikakken bayani recreation da lamarin ba. Wannan sabon harin ya kawo adadin ofisoshin hukumar da aka kona zuwa 23. Wannan na zuwa makonni bayan da wasu ‘yan daba suka lalata ofisoshin hukumar a Akwa Ibom da Abiya da Anambra da Inugu da Imo.

- Advertisement -