CHAMPIONS LEAGUE: Chelsea Da Manchester City Za Su Kece Raini A Portugal

- Advertisement -

CHAMPIONS LEAGUE: Chelsea Da Manchester City Za Su Kece Raini A Portugal

Hukumar kula da wasannin nahiyar turai ta Eufa tace za’a gudanar da wasan karshe na cin kofin zakarun turai na Champions League tsakanin Chelsea da Manchester City a Portugal inda ‘yan kallo mutum dubu 6,000 daga kowacce kungiya za su halarce shi.

Wasan da za a fafata ranar 29 ga watan Mayu, an mayar da shi birnin Porto na kasar Portugal daga kasar Turkiyya sakamakon kullen korona kuma filin wasan na FC Porto yana iya daukar mutum 50,033

Portugal na cikin kasashen da Ingila ta kyale ‘yan kasarta su je domin haka ‘yan kwallo da magoya bayansu za su iya zuwa ba tare da an killace su idan suka koma gida ba a cewar hukumomin kasar.

kasar Turkiyya dai na cikin kasashen da Birtaniya ta dakatar da ‘yan kasarta daga zuwa kuma wannan ce shekara ta biyu da za a yi wasan karshe na gasar ta Champions League a kasar ta Portugal.

“Ba za mu hana magoya baya zuwa kallo kafa-da-kafa ba kuma ina farin ciki da aka samu matsaya domin haka ya nuna cewa nan gaba kadan magoya baya zasu koma fili domin ci gaba da kallo,” in ji shugaban Uefa Aleksander Ceferin.

Uefa da jami’an gwamnatin Birtaniya da kua na hukumar kwallon birtaniya solar tattauna kan yiwuwar yin wasan a filin wasa na Wembley sai dai an gaza cimma matsaya kan batun killlace manyan mutane, da masu daukar nauyin gasar da ‘yan jarida.

- Advertisement -