CBN Zai Wanzar Da Tsarin Samar Da Kudaden Musaya Don Dakile Shigo Da Madara

0
62

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya sanar da cewa, nan bada jimawa zai wanzar da tsarin samar da kudaden musaya na kasar waje don dakile shigo da madara cikin kasar nan, inda bankin ya kara da cewa, Nijeriya ta kai matsayin da zata iya samar da wadatacciyar madarar a cikin kasar nan.

Bugu da kari, masu sarrafa madara a cikin Nijeriya sunyi nuni da cewa, za’ a iya karya kwarin gwaiwar shigo da madara cikin Nijeriya ne kawai idan gwamnatin tarayya ta kara kudin fiton shigo da itazuwa kashi 25 a cikin dari.
Gwamnan Babban Bankin na Nijeriya Godwin Emefiele ne ya sanar da hakan a wata ganawar da ya yi da manema labarai a Abuja.

CBN Zai Wanzar Da Tsarin Samar Da Kudaden Musaya Don Dakile Shigo Da Madara

A cewar Gwamnan Babban Bankin na Nijeriya Godwin Emefiele, barin ana shigo da madarra cikin kasar nan yana kara janyo mata koma baya, inda kuma hakan ke janyo nakasu ga masu sarrafa a cikin Nijeriya.

Gwamnan Babban Bankin na Nijeriya Godwin Emefiele yaci gaba da cewa, duk wanda keda ra;ayin samar da wajen yin kiwon shanu bankin zai tallafa masa da bashi da kuma samar masu da kayan aikin saffara madarar.

Gwamnan Babban Bankin na Nijeriya Godwin Emefiele ya kara da cewa, Nijeriya ta shafe shekaru sama da 60 tana shigo d madara a cikin kasar nan.

Sai dai, a hirra sa manema labarai, Manajin Darakta na kamfanin sarrafa madara na L &Z Yoghurt dake a jihar Kano Alhaji MD Abubakar ya yi nuni da cewa, dakatar da samar da kudaden musayar bazai karyawa masu sarrafa ta kwarin gwiwa ba.

Manajin Darakta na kamfanin Alhaji Abubakar ya kara da cewa, gibin dake a tsakanin kudaden musayar na kasar waje da kuma kasuwar cikin gida ba zai isa a hana shigo da madarra cikin kasar nan ba.

KU KARANTA: Za Mu Cigaba Da Gudanar Da Taron Bajekolin Noman Albasa

Alhaji Abubakar ya buga misali da kasar Kenya da take da kashi 60 a cikin dari na kudin shigo da kaya cikin kasar data kakabawa masu shigo da madara cikin kasar ta, inda kuma ya yi nuni da cewa, kashi 15 a cikin dari ana yin amfani dasu ne wajen bunkasa fannin samar da madara.

Shi kuwa wani mai samar da madara a jihar Kwara Ayodotun Ismail, ya goyi bayan ra’ayin Manajin Darakta na kamfanin Alhaji Abubakar.

What's On Your Mind?