Bunkasuwar Tattalin Arzikin Sin Da Kara Bude Kofarta Sun Janyo Karuwar Jarin Waje

0
51

Bunkasuwar Tattalin Arzikin Sin Da Kara Bude Kofarta Sun Janyo Karuwar Jarin Waje

Daga CRI Hausa

Jami’in kungiyar hadin gwiwar tattalin arziki na OECD ya ce, hasashen samun kyakkyawar makoma na bunkasar tattalin arzikin kasar Sin, da manufofin kara bude kofar kasar ga ketare, solar kasance a matsayin manyan jigogin da suka janyo jarin waje na kai tsaye a kasar Sin.

Jarin waje da kasar Sin ta samu ya karu da kashi 14 bisa 100 a shekarar bara, lamarin da ya baiwa kasar damar zama sahun gaba a duniya, a cewar Margit Molnar, shugabar kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin ta OECD reshen kasar Sin, ta bayyana hakan ne a zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Haka zalika, jarin wajen kai tsaye wato FDI na duniya ya ragu da kashi 38 bisa 100 a shekarar 2020 zuwa dala biliyan 846, mataki mafi kasa tun a shekarar 2005, kamar yadda alkaluman da kungiyar tattalin arzikin mai babban ofishinta a birnin Paris ta fitar a ranar Juma’a.

Kasar Sin ta zarce Amurka a matsayin kasar da ta fi samun karuwar FDI mafi yawa a duniya a shekarar da ta gabata, yayin da manyan kasashen biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya suka samu FDI da ya kai dala biliyan 212 da dala biliyan 177.(Mai fassarawa: Ahmad daga CRI Hausa)

What's On Your Mind?