Bunkasa Rayuwar Al’ummar Karamar Hukumar Sabon Gari Shi Ne Babban Buri Na— Hon Shaka

0
105

Bunkasa Rayuwar Al’ummar Karamar Hukumar Sabon Gari Shi Ne Babban Buri Na— Hon Shaka

A ranar 5 ga watan Afrilu ne ake sa ran za a gudanar da zaben fidda da gwani na masu neman kujerar karamar hukumar Sabon Gari a jihar Kaduna, cikin wadanda suke gaba masu neman kujerar solar hada Hon.

Yusuf Salihu Shaka, yana kuma daya daga cikin wanda ya samu kabuwa a wajne al’umma musamman matasa, hakan kuma ya faruwa ne sdaboda matakai na taikamawa da Hon Shaka yi ga matasa a yankin a cikin shekarun da suka gabata, Editanmu, Bello Hamza ya samu tattaunawa da shi, in da ya bayyana sirrin da ke tattare da irin farin jininsa a karamar hukumar Sabon Gari da kuma irin ayyukan alhairi da ya shirya gabatarwa in Allah ya kai shi ga zama shugaban kamarar hukumar Sabon Gari, ga dai yadda hirar ta kasance.

Salam Alaikum, ranka ya dade zamu so ka gabatar mana da kanka.
Toh sunana Yusuf Salihu, wanda aka fi sani da suna Shaka. Ina takarar gujeran shugabancin karamar hukumar Sabon Gari ne a karkashin jam’iyyar APC.

Ganin cewa wannan ba shi ne fitowarka na farko ba, wani ayyuka ka gabatar ma al’ummar karamar hukumar Sabon Gari wanda kake ganin ya cancanta a wannan karon su jajirce su tabbatar da solar zabe ka a matsayin Shugaban karamar hukumar.

Yadda Mace Ya Kamata Ta Kasance A Wajen Mijinta

Ai tun fitowar da nake yi na farko mutanen karamar hukumar Sabon Gari suna tare da ni. Kuma basu taba kin zabe na ba sai dai a samu. Maslaha can da nan a hakura. Ko kuma jamiyya mai mulki ta rike kujerar. Amma duk zaben da na fito ba wanda na yi na rashin nasara a cikin sa. Wannan ma muna sa ran cewa duk da muna jam’iyya daya da chairman mai ci, shima in Allah ya yarda zamu kai shi kasa.

Baku ganin cewa takarar da zaka yi da Shugaban karamar hukuma mai ci a cikin jam’iyyar ku, baka tunanin wani barazana ko dardar akan fuskantar shi?
Wallahi ko daya, wancan karo ma yana kantoma, sai a ofishin Gwamna aka bada hakuri sannan na hakura na janye masa. To kaga wannan kuma ba maganan a ce 9 za a ba hakuri, ko ya hakura ko kuma yazo mu buga. Ni dai nasan ina tare da talakawa. Saboda na nema masu aiki,na nema masu scholarship, na nema masu gyaran gidaje, na kula masu da harkar lafiya. Nasan insha Allah talakawan Sabon Gari suna tare da ni.

Toh ita shugabanin jam’iyyar APC, kana tunanin samun adalci daga jamiyya?

Toh Alhamdulillahi baza’a ce baza’a samu adalci ba. Indai basu yi mana adalci ba akwai inda yakama mu kai. Amma kuma bama tunanin cewa tunda interim ne, bama tunanin cewa sune zasu gabatar da komai da komai. Akwai dai yadda dai za’ayi in Allah ya yarda.

Toh me ka tanadar ma Al’ummar karamar hukumar Sabon Gari na ayyaukan cigaba idan Allah ya tabbatar maka da wannan buri naka?
Toh, sanin kowa ne dai mutanen karamar hukumar Sabon Gari solar san cewa muna kula da bangaren ilimi da aljihun mu, muna kula da bangaren gudajen su,muna kula masu da Empowerment, ma’na bada jari da sauransu zuwa abubuwan hawa da sauransu. Duk muna yi masu wannan. Wanan karon in Allah ya sa abun da dai suka sani dai, suka san gidanmu akai shine zamu cigaba dashi, InshaAllah.

Matasa da Mata fa, me ka tanadar masu?

Toh matasa da mata, solar wadannan Kaman ya ya ne a wuri na, Mata kuma iyaye ne a wurinmu. A yanzu haka baka baka mutum hamsin zuwa saba’in. Wanda na sama wa, police, Naby, airforce, da Military. Da kuna wanda na tura Abuja suna nan suna aiki a fadar shugaban kasa. Toh mata kuma mun dangerous a dama tallafi, mun taimaka masu wajen bayar da sana’oi da sauransu, mun tallafa masu a jari haka. To komai dai yana tafiya dai dai insha Allah.

Toh wani kira kake dashi ga ‘yan jam’iyyar APC a matakin farko? musamman ganin cewa zaben fidda gwani yana nan tafe.

Toh, wayau dai aka ce yasan naki, Ina Kira ga yan jam’iyyar APC, shekara uku dai ba kwana uku bane, solar yi kuma solar kara yi. Shekarar solar hudu kenan da rabi harda kantoma da aka basu. In akwai abun da zasu fito suyi tallan kansu a wurin su, to su duba, in kuma Babu to suyi hakuri su wannan dama mu kuma su ga irin abun da zamu tabbatar masu Dashi.

Ranka ya dade, ko akwai wani kira da kake dashi Wanda ban tambaye ka ba wanda kake so ka isar ma al’umma?
To kiran na shi ne zuwa ga gwamnatin jihar Kaduna ne, ta duba Allah ta tsaya ta yi adalci, wanda yake da jama’a, aba shi zaben shi. Shine maganan da zan yi. In kuma za a bada wani hakuri ne, to wancan karon ni aka ba hakuri wannan karon kuma yakamata sune za su yi hakuri, ni kuma a ga irin kamun nawa ludayin.

Ranka ya dade mun gode, Allah ya tabbatar da alkhair
Nima na gode kwarai da gaske

What's On Your Mind?