Buhun shinkafa ya koma N19,000, masu boye kayan abinci sun shiga Uku

0
126

Buhun shinkafa ya koma N19,000, masu boye kayan abinci sun shiga Uku

Masu tara kayan abinci suna boyewa domin sayar wa da tsada sun shiga uku domin kuwa kungiyar masu sarrafa shinkafa ta Nigeria, “Rice Processors Affiliation of Nigeria”, RIPAN, ta ce amince ta karya farashin shinkafa zuwa Naira Dubu Goma Sha Tara, (50kg a N19,000)

Martani ga Garba Shehu Daga mawaki Ado Gwanja Kan Furucin Kashe manoma a Borno

Manuniya ta ruwaito sabon farashin zai fara aiki ne daga ranar 14 ga watan Disamba da muke ciki.

Babban jami’in RIPAN, Aminu Ahmed ya shaidawa jaridar Every day Nigerian cewa hakan na zuwa ne bayan ganawarsu da Babban Bankin Nigerian CBN, a wani mataki na rage radadin talauci da tsadar kayan abinci a Nigeria.

Manuniya ta ruwaito farashin buhun shinkafa a yanzu yana kaiwa daga N28,000, zuwa N35,000 ko ma fiye da haka.

What's On Your Mind?