Buhari Ya Yi Alkawarin Daukar Mataki Kan Barazanar ‘Yan Bindiga Ga Samar Da Abinci

- Advertisement -

Buhari Ya Yi Alkawarin Daukar Mataki Kan Barazanar ‘Yan Bindiga Ga Samar Da Abinci

Ya Roki ‘Yan Nijeriya Da Su kara Fahimtar Yanayin Matsalar Tsaro

Daga Mahdi M. Muhammad,

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayar da tabbacin cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da dukkan karfin arzikin da ke akwai wajen kawar da ‘yan bindiga don tabbatar da samun damar shiga gonaki da noman abinci a cikin kaka mai zuwa.

Shugaban kasar, a cewar wata sanarwa daga babban hadiminsa na musamman kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya yi kiran ne a wata tattaunawa da manema labarai na fadar Shugaban kasa jim kadan bayan ya idar da Sallar Idi-fitr a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja, don bikin katamar Sallah da ke numa karshen azumin Ramadana mai tsawon wata, ranar Alhamis.

A cewarsa, za a magance matsalar ‘yan bindiga da masu satar mutane don tabbatar da cewa kasar ba ta fuskantar barazanar wadatar abinci.

Shugaban, wanda ya yi fatan samun damina mai albarka a wannan shekarar, ya ce, “jami’an tsaro na aiki tukuru don dawo da karfin gwiwa a kan ‘yan bindiga, ta yadda za mu koma cikin kasar.”

“Wannan yana da matukar muhimmanci. Wannan shine abin da hukumomin ke aiki yanzu. Muna son mutane su koma kasar ta yadda za mu samu wadataccen abinci ga kasar har ma da fitar da shi,” in ji shi.

Yayin da yake bayyana kokarin da ake yi na shawo kan matsalar tsaro a kasar nan daga bangaren gwamnati, Buhari ya ja hankali kan jerin dogayen tarukan da aka gudanar a makonnin da suka gabata, wanda ya jagoranta, yana mai cewa, mai ba da shawara kan sha’anin tsaro da kuma wani bangare na kudurorin wasu kuma solar rufawa kansu asiri.

“Tare da albarkatu da ma’aikata da muke da su, muna aiki tukuru. Muna kuma fatan ‘yan Nijeriya za su fahimci matsalar. ‘Yan Nijeriya solar san a wane mataki muka zo a cikin 2015, wace kuma muke a yanzu ta fuskar tsaro da tattalin arziki kuma muna iyakar kokarinmu,” inji shi.

Shugaban ya yaba wa Majalisar Dokoki ta kasa kan goyon bayan da ta ba shi, yana mai cewa Majalisar Dokoki ta kasa tana ba da hadin kai sosai.

Ya ce “Cikin abubuwan da suke akwai, hakika suna ba mu fifiko kan bukatunmu na soji.”

Duk da haka, ya yi kira ga fitattun ‘yan kasa da su nuna kyakkyawan yabo recreation da matsalolin da kasar ke fuskanta.

“Ya kamata manyan mutane su yi kakarin fahimtar yanayin sojoji,” in ji shi.

Ya ce, “Idan muka yi oda don makamai da motocin sulke, yana daukar lokaci don masana’antun su gama.”

“Yana daukar lokaci kafin a tura su sannan idan an kawo su daga karshe, ana kai su cibiyoyin horo, su horar da masu horarwar kafin a tura su filin. Wannan aiki ne mai matukar tsawo,” in ji shi.

Shugaban ya kuma roki ‘yan Nijeriya da su kara fahimta kan halin tsaro da kasar ke ciki a yanzu.

Ya kuma buaaci fitattun ‘yan Nijeriya da su nuna kyakkyawan yabo ga matsalolin da kasar ke fuskanta.

Buhari ya kasance yana fuskantar matsin lamba daga ‘yan Nijeriya kan neman mafita mai dorewa ga mafi munin kalubalen tsaro a kasar tun samun ‘yancin kai.

Ya ce, “Ina sa ran ‘yan Nijeriya za su kara fahimta a kan batutuwan da abin ya shafa, duba lokaci da kuma kayayyakin da ake da su. Misali, lokacin da muka shigo, a yankin Arewa maso Gabas, ka tambayi mutane a jihohin Adamawa da Borno da Kudu maso Kudu dangane da tsaro. Ba tare da tsaro ba, ba za ku iya yin komai ba. Babban abin mamakinmu da takaicinmu shine abinda ke faruwa a Arewa maso Yamma kuma muna magance shi,” in ji shi.

Ya kara da cewa, “Yakamata manyan mutane su yi kokarin fahimtar da sojoji. Idan muka yi odar makamai da motoci masu sulke, yana daukar lokaci kafin masana’antun su gama. Yana daukar lokaci kafin a tura su sannan idan an kawo su daga karshe, ana kai su cibiyoyin horo, su horar da masu horarwar kafin a tura su filin. Wannan aiki ne mai matukar tsawo.”

Shugaba Buhari ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa gwamnatinsa za ta yi amfani da duk karfin da ke akwai da kuma karfin ma’aikata wajen tunkarar ‘yan bindiga da sauran masu aikata barna a sassa da dama na kasar.

- Advertisement -