Buhari Ya Sake Ganawa Da Shugabannin Tsaro A Fadarsa Aso Rock

- Advertisement -

Buhari Ya Sake Ganawa Da Shugabannin Tsaro A Fadarsa Aso Rock

Daga Mahdi M. Muhammad,

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci wani taron majalisar tsaro a fadar shugaban kasa da ke Abuja, jiya Talata.

Wannan shi ne karo na biyu da ya yi irin wannan ganawa da shugabannin tsaro a kasa da kwanaki hudu.

An kira taron farko ne a ranar Juma’ar da ta gabata.

Taron na ranar Talata, wanda aka gudanar a dakin taro na Uwargidan Shugaban kasa a gidan Gwamnatin, ya samu halartar Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, da Shugaban Ma’aikatan fadar Shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari.

Sauran wadanda suka halarci taron solar hada da Ministan tsaro, Manjo-Janar Bashir Magashi (mai ritaya), mai ba da shawara kan harkokin tsaro, Manjo Janar Babagana Monguno (mai ritaya), babban hafsan tsaro, Janar Fortunate Irabor, Shugaban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, Shugaban hafsan sojojin ruwa, bice Admiral Awwal Zubairu, Shugaban hafsan sojin sama, Air Marshal Isiaka Amoo, da mukaddashin Sufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Usman Baba.

Babu wani bayani da aka gabatar bayan taron kuma babu wata sanarwa da aka fitar kawo yanzu sport da sakamakonta.

Duk da haka, bayan taron na ranar Juma’ar da ta gabata, mai ba Shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro ya ce, Shugaba Buhari, wanda ya damu da yadda ake ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro a sassan kasar, ya kira wani muhimmin taro na Kwamitin tsaron kasa yayin da yake ci gaba da fuskantar halin da ake ciki.

Monguno ya ce, Shugaban ya bayyana a wurin taron cewa, yayin da masu tayar da kayar baya, ‘yan bindiga da masu laifi suke har yanzu, ba shi da wata shakku cewa hukumomin tsaron Nijeriya za su shawo kan duk matsalolin tsaro da ake fuskanta a yanzu kuma za su fatattaki rundunonin ‘yan ta’addan da ke yawo a sassa daban-daban na kasar.

“Yayin da masu laifin suka ci gaba da gwada nufin gwamnatin Nijeriya, Shugaban kasa da Majalisar wadanda suka gudanar da muhimmiyar taron yau har zuwa safiyar Talata don karbar karin bayani daga shugabannin tsaro, an shirya kuma solar yanke shawarar kawo karshen cin zarafin da ake yi wa al’ummar kasar wajen yin duk abin da dace,” in ji shi.

Ya ce, “Shugaban kasa ya shirya tsaf don daukar kwararan matakai sport da babbar maslaha ta mutane da kuma kasar Nijeriya.

Sanarwar ta ce, “ba za a sake yin hakan ba har sai an maido da zaman lafiya da tsaro a cikin yankunan mu.”

- Advertisement -