Buhari Ya Sake Dakatar Da Kai Masa Gaisuwar Barka Da Sallah

- Advertisement -

Buhari Ya Sake Dakatar Da Kai Masa Gaisuwar Barka Da Sallah

Daga Mahdi M. Muhammad, Abuja

 

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sake cewa ba zai karbi gaisuwar barka da Sallah ba a matsayin wani bangare na ayyukan nuna karshen watan Ramadan daga mutanen da ke ziyartarsa a fadarsa.

 

Ya nemi cewa shugabannin addinai, na gari, da na siyasa wadanda yawanci suke yi masa girmamawa ta gargajiya su kasance masu gamsuwa da bukukuwa na gari a cikin gida dangane da annobar COBID-19.

 

Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi mai taken ‘Shugaba Buhari wajen gudanar da bikin Idi a Billa, yana shirin yin biki a cikin gida.’

 

Al’ada ce a yayin manyan bukukuwan addini, Mataimakin Shugaban kasa yana jagorantar Ministan babban birnin tarayya da sauran shugabanni da mazauna Abuja don yi wa Shugaban kasa mubaya’a a cikin fadar Shugaban kasa.

 

Buhari ya ci gaba da al’adar har zuwa shekarar da ta gabata lokacin da aka ayyana takunkumi kan yawan mutanen da za su iya taruwa saboda annobar COBID-19.

 

A cikin sanarwar a ranar Lahadi, Shehu ya ce, Buhari ba zai karbi gaisuwar Sallah ba kamar yadda ya samu a shekarar da ta gabata.

 

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “kamar yadda Musulmai a Nijeriya suka hada kai da sauran mutane a duniya a shirye-shiryen bikin Eid Al-Fitr, ranar da ake yin ta don nuna karshen watan Ramadan, watan azumi, Shugaba Buhari ya ba da umarnin cewa a takaita dukkan bukukuwa saboda annobar Korona ta da addabi kasashen duniya.

 

“Don haka, Shugaban kasar, Iyalinsa, masu taimaka masa, mambobin majalisar zartarwa da Shugabannin ma’aikata wadanda suka zabi ci gaba da zama a Abuja za su hallara cikin cikakkiyar yarjejeniya ta COBID-19 a farfajiyar Fadar Shugaban kasa don gudanar da Sallar Idi. Lokaci da aka kayyade domin sallah ya kasance 9.00 na secure,” in ji sanarwar.

 

Sanarwar ta kara da cewa, “bayan haka, ba bu wata girmamawa ta gargajiya da za a yi wa Shugaban kasa daga shugabannin addini, na gari da na siyasa. Kamar yadda ya faru a shekarar da ta gabata, Shugaban ya karfafa wa irin wadannan shugabanni gwiwa da su gamsu da bukukuwan da suka dace a cikin gida saboda annobar.”

 

“Shugaba Buhari yana mika godiya ta musamman ga Ulama Malaman addinin musulunci da duk sauran shugabannin addini, Musulmi da Kirista, wadanda ke ci gaba da yi wa kasa da al’ummarta addu’ar alheri.”

 

A cewar sanarwar, Buhari ya kuma yi amfani da damar wajen jajantawa duk wadanda suka rasa ‘yan uwansu saboda abin da ya bayyana da hauka da ke faruwa a sassan kasar.

 

Shehu ya nakalto shi yana kira ga dukkan shugabannin yankin da su tattauna da matasan su tare da gargadin su kan amfani da su wajen tayar da fitina.

 

Ya ce, “Idan muka kai hari kan cibiyoyin da ke tsaron mu, wa zai kare mu a cikin gaggawa na nan gaba?”

- Advertisement -