Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a fitar wa hukumar kidaya ta kasa watau NPC, kudi domin aikin EAD a wasu bangarorin Najeriya.
The Nation ta ce Mai girma Muhammadu Buhari ya bada umarnin a warewa hukumar NPC Naira biliyan 10 domin kidaya a kananan hukumomi 546.
Ana yin wannan aiki na EAD ne domin a tsara yadda za a ji dadin kidaya mutanen da ke Najeriya.
Haka zalika shugaban kasar ya bada umarni a ware Naira biliyan 4.5 a kasafin kudin shekara mai zuwa domin ayi aikin kidayar mutanen da ke kasar nan.
Buhari ya amince da fitar da biliyan 10 domin kidaya
Mukaddashin shugaban NPC na kasa, Dr. Eyitayo Oyetunji, ya shaidawa ‘yan jarida wannan lamari a safiyar ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba, 2020.
Dazu ne a hedikwatar hukumar NPC, Dr. Eyitayo Oyetunji ya yi wa manema labarai bayanin inda aka kwana sport da aikin sharar fagen kidayar da za ayi.
“Shugaban kasa ya bada umarnin a sa Naira biliyan 4.5 a cikin kasafin kudin 2021 domin kammala wannan aiki a shirin kidayar da za ayi.” Inji Oyetunji.
“Babu shakka wannan gagarumar nasara ce da aka samu a gwamnatin shugaba Buhari, ta fahimci amfanin alkaluma, musamman adadin ‘yan kasa.”
Ya ce adadin yawan ‘yan Najeriya ya na da muhimmanci wajen tsare-tsare da kason arzikin kasa.
Dazu mun kawo maku karin bayanai sport da abin da ya sa duka Jihohi su ka maka Shugaban kasa a kotu, su na kukan Buhari ya toye masu hakkinsu.
Wasu Lauyoyi solar bayyana makasudin da ya sa Gwamnoni su ka yi wa Buhari fito-na-fito.
144 total views, 1 views today
Be the first to comment