Buhari ya assasa tubalin ginin Jami’ar Kungiyar JIBWIS a Jigawa

0
151
  • Shugaba ƙasa Muhammadu Buhari ya assasa tubalin ginin Jami’ar Musulunci a jihar Jigawa

  • Ministan Sadarwa Datka Isa Pantami ne ya wakilci Shugaba Muhammadu Buhari wurin taron

  • Taron ya samu hallarcin gwamnoni, ƴan majalisa, masu sarautun gargajiya, manyan ma’aikatan gwamnati da sauransu

Buhari ya assasa tubalin ginin Jami'ar Kungiyar JIBWIS a Jigawa

Shugaba Muhammadu Buhari ya assasa tubalin ginin jami’ar musulunci ta As-Salam World College, Hadejia, mallakar kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’ah Wa’iqamatis Sunnah, JIBWIS, jihar Jigawa.

Shugaban ƙasar da ministan sadarwa , Dakta Isa Pantami ya wakilta ya assasa tubalin ginin jami’ar a wurin taron.

Buhari shine baƙo na musamman wurin taron yayin da Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’advert Abubakar shine shugaban taron.

Kazalika, gwamnonin da suka hallarci taron solar hada da Muhammadu Badaru na jihar Jigawa da gwamnonin Sokoto, Kebbi, Katsina, Kano da tsaffin gwamnonin Zamfara.

Kazalika, ƴan majalisa, masu sarautun gargajiya, shugabannin addini, manyan ma’aikatan gwamnati da masu tallafawa al’umma solar hallarci taron.

SO BAKIN CIKI: Wani Mutum Ne Ya Buge Saboda Kudi Da Wayarsa (Hotuna)

Da ya ke jawabi wurin taron, shugaban JIBWIS na ƙasa, Sheikh Bala Lau ya sake jaddada cewa jami’ar ta al’ummar musulmi ce.

Ya ce: “Hakan yasa muke gayyatar musulmi a duk inda suke su zo su taimaka da duk abinda Allah ya sawwake musu.”

“A yayin da muke fara wannan katafaren aikin, kowa ya sani cewa fatan mu shine kafa jami’ar ingantacciya da za ta amfani dukkan al’ummar musulmi. Da fatan Allah ya mana jagora. Amin.”

A wani labarin daban, Alhaji Tanko Yakasai a ranar Litinin ya ce shugaban kasa, Muhammadu Buhari ba shi da ikon sauya fasalin tsarin mulkin Najeriya a karkashin kundin tsarin mulkin kasar.

Ya shawarci masu neman ganin an yi wa tsarin mulkin kasar garambawul su tabbatar wakilansu a majalisun jihohi da tarayya solar samar da dokokin da za su bada daman sauya mulkin kasar.

What's On Your Mind?