Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai

0
107

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince a dauki daliban NCE aikin gwamnati kai tsaye da zaran solar kammala karatun su.

Ministan ilimi, Alhaji Adamu Adamu a ranar Litinin, 5 ga watan Oktoba ya bayyana hakan, a babban birnin tarayya Abuja, yayin bukin murnar zagayowar ranar malamai ta duniya.

Buhari ya amince a bawa daliban da suka yi karatun NCE aiki, ya kara shekarun aikin malamai

2023: Atiku ya magantu a kan fastocin yakin neman zabensa

Haka zalika, shugaban kasar ya amince da bayar da gurbin karatu na kai tsaye tare da daukar nauyin karatun ‘ya’yan malamai.

Shugaban kasar, ya kuma bayar da umurni da a kara kudin albashin malaman makarantar tare da tsawaita shekarun aikin su.

Legit.ng Hausa ta ruwaito maku cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amice da karin albashi ga malaman makaranta, ya sanar da hakan a murnar ranar malamai ta duniya.

Shugaban kasar ya kara wa’adin shekarun aikin malaman daga 35 zuwa 40, yayin da ya ke albishir da kara albashin malaman don basu kwarin guiwar gudanar da ayyukansu.

A wani labarin, Sashen kula da huldodin jama’a na rundunar ‘yan sandan Nigeria ya samar da lambobin waya da kafofin dandalin sada zumunta da WhatsApp domin tabbatar da tsaftataccen aiki a rundunar.

Rahotanni solar bayyana cewa, rundunar ta samar da wadannan hanyoyin ne domin yin nazari da sa ido ga ayyukan sashen FSARS da sauran jami’an kwantar da tarzoma da ke cikin ta.

What's On Your Mind?