Buhari ya ƙarawa malamai albashi mai tsoka da shekarun aiki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya amince da biyan albashi na musamman ga malamai.

Shugaban kasar ya kuma kara wa’adin shekarun aikin malamai daga shekaru 35 zuwa 40, jaridar This Day ta ruwaito.

Ministan ilimi, Adamu Adamu, ne ya sanar da hakan a yau Litinin, 5 ga watan Oktoba.

Ya bayar da sanarwar ne a cikin wani jawabi na musamman da ya karanto yayinda yake wakiltan shugaban kasar a wajen taron zagayowar ranar malamai ta duniya.

Buhari ya ƙarawa malamai albashi mai tsoka da shekarun aiki

Zuwa yanzu dai ba a san yadda tsarin zai kasance ba.

A wani labarin kuma, Sunday Dare, ministan matasa da bunkasa wasanni, ya ce gwamnatin tarayya karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari na shirin daukar matasa miliyan daya aiki.

Dare ya bayyana hakan ne a ranar Juma’ar makon da ya gabata, a yayin wani bukin baje kolin kasuwanci na fasahar matasa a babban birnin tarayya Abuja.

Ma’aikatar matasa da bunkasa wasanni tare da hadin guiwar gidauniyar ‘I Select Life’ (na zabi rayuwa) suka shirya taron.

An shirya taron ne domin bukin murnar cikar Nigeria shekaru 60 da samun ‘yanci, da kuma taya matasa murna kan nasarar da suka samu a kasuwanci, kirkira, aikin hannu da fasahar zamani.

Rundunar ‘yan sanda ta samar da lambobin kira idan jami’anta sun ci zarafin ka

Taken taron shi ne, ‘Mafarkin kasata Nigeria,’ kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

A cewar Dare, ma’aikata matasa da bunkasa wasanni na hada karfi da karfe da sauran ma’aikatu don samar da ayyukan yi, lamarin da zai tabbata kafin karshen watan Oktoba.

 133 total views,  2 views today

About M. Jamiu 416 Articles
Hausa News Editor & Sport Director

Be the first to comment

Leave a Reply