Buhari Na Jagorantar Taron Majalisar Tsaro Ta Kasa

0
101

Buhari Na Jagorantar Taron Majalisar Tsaro Ta Kasa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yanzu haka yana jagorantar taron majalisar tsaro ta kasa (NSC) a fadarsa da ke Abuja.

Ganawar na zuwa ne sakamakon karuwar matsalolin tsaro a yankuna daban-daban na kasar nan da kuma korafin da masu ruwa da tsaki da dama keyi tare da kira ga shugaban kasa da ya dauki matakin gaggawa.

Wadanda suka halarci taron solar hada da Mataimakin Shugaban Kasa,Yemi Osinbajo; Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Mista Boss Mustapha; shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari; da kuma mai bada shawara kan harkokin tsaro (NSA), Manjo-Janar Babagana Monguno (rtd).

Sauran solar hada da Babban shugaban Hafsan soja(CDS), Janar Fortunate Irabor; Shugaban hafsin soji, Laftana-Janar Ibrahim Attahiru; Shugaban hafsan sojojin ruwa, Vice Admiral Awwal Zubairu; Shugaban hafsan sojojin sama, Air Marshal Ishiaka Oladayo Amoo.

Mukaddashin Sufeto-janar na ‘yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba shi ma ya halarci taron.

What's On Your Mind?