Buffon Ya Yi Hannun Riga Da Juventus

- Advertisement -

Buffon Ya Yi Hannun Riga Da Juventus

Shahararren mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Gianluigi Buffon ya ce zai yi hannun riga da kungiyar da ke wasa a Serie A ta Italiya a karshen wannan kakar ta bana da ake kokarin karkarewa.

Buffon, mai shekaru 43 a duniya, ya lashe kofunan Serie A har guda 10 da na kalubalen Italiya guda four a zamansa da Juventus sau biyu bayan da ya dawo kungiyar Juventus daga kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German a shekarar 2019 bayan shafe kakanni 2.

Mai tsaron ragar ya shaida wa manema labarai cewa lokaci ya yi, saboda haka kamata ya yi ya bar kungiyar domin ya bawa matasan ‘yan wasa dama suma su gwada sa’arsu a kungiyar ta Juventus.

Buffon, wanda ya lashe kofin duniya da Italiya a shekarar 2006 ya kara da cewa dayan biyu ne, ko ya hakura da harkar kwallon kafa kacokan, ko kuma idan ya samu inda ya ba shi sha’awa ya dan buga wasa, yana mai cewa a ganinsa ya yi duk abin da zai yi a Juventus, kuma ya samu duk abin da yake bukata a kungiyar.

Tsohon dan wasan tawagar Italiyar ya buga mata wasanni 176 a matakin kasa da kasa, kuma shine ya kafa tarihin dan wasan da ya fi kowanne buga wasanni a gasar Serie A da wasanni 656.

 

- Advertisement -