Budurwa ta rasu kwanaki biyar kafin daura mata aure

0
73

Wata budurwa yar kasar kamaru da ke karatun zama ma’aikaciyar jinya, Petra Nji ta rasu a hatsarin mota kwanaki biyar kafin a daura mata aure.

Petra da mijin da za ta aura, Isbias Forsack suna hanyarsu ta dawowa daga Douala ne bayan zuwa daukan hotunan kafin aurensu inda hatsarin ya ritsa da su a kan titin Tiko-Douala a ranar Litinin, 11 ga watan Janairun 2021.

Isbias da sauran fasinjojin da ke cikin motar solar samu raunuka daban-daban kuma an garzaya da su zuwa wani asbiti da ke kusa amma ita Petra ta mutu.

Daga Karshe Daurawa Yayi Magana Akan Hukuncin P.O.S Fahimta Ta Akan Sana’ar P.O.S !!

An shirya yin auren su na coci ne a ranar Asabar 15 ga watan Janairu a cocin Presbyterian da ke Molyko yayin da auren gargajiya kuma za a daura a ranar Juma’a 15 ga watan Janairu.

KU KARANTA: Mutumin da budurwarsa ta cinnawa wuta a Benue ya mutu

Wasu kawayen amaryar solar sanar da rasuwarta a shafinsu na dandalin sada zumunta na Fb inda suka yi mata addu’ar samun rahamar Ubangiji tare da yi wa yan uwanta ta’aziyyar rasuwarta.

A wani labarin daban, kun ji kungiyar samari masu kishin aljihunsu da ake kira Stingy Males Affiliation (SMAN) a turance tana samun bunkasa inda ake ta bude rassa a kasashen duniya daban-daban, BBC Hausa ta ruwaito.

A ranar Litinin 11 ga watan Janairu ne kungiyar ta bude shafinta na musamman a kafar Twitter da Fb tare da tamburi a Najeriya.

Wasu kasashen Afirka solar bi sahun Najeriya solar bude rassan kungiyar a kasashensu, kasashen solar hada da Ghana, Liberia, Uganda, Malawi da Zambia.

What's On Your Mind?