BUA Ya Gwangwaje Wata Jami’a Da Kyautar Naira Bliyan 1

0
129

BUA Ya Gwangwaje Wata Jami’a Da Kyautar Naira Bliyan 1

Daga Rabiu Ali Indabawa

Shugaban kamfanin BUA, Abdul-Samad Isyaka Rabi’u, ya ba da kyautar kudi Naira biliyan 1 ga jami’ar Ibadan (UI) domin gudanar da gyara a bangarori daban-daban na jami’ar. Gidauniyar shugaban na ware makudan kudade a duk shekara domin tallafa wa jama’a ta kangaren lafiya, ilimi da kuma cigaba. Daraktan dake kula da alakar Kamfanin da gwamnati, wanda shi ne ya wakilci shugaban, ya ce wannan gidauniyar na ware Dala miliyan 100 domin tallafa wa jama’ar Nijeriya da kuma Africa. Shugaban BUA, Alhaji Abdul-samad Rabi’u ne ya bada kyautar wannan zunzurutun kudi Naira biliyan 1 ga jami’ar Ibadan (UI) domin gyaran makarantar, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Alhaji Rabi’u ya ba da kyautar ne a wata ziyara da ya kai ofishin mukaddashin shugaban makarantar, Farfesa Adebola Babatunde Ekanola, karshen mako. Alhaji Rabiu, wanda daraktan alakar gwamnati a kamfanin BUA, Dakta Aliyu Idi Hong, ya wakilta ya ce an bai wa jami’ar wannan kyautar kudinne saboda yadda take gudanar da ayyukanta masu kyau.
“Shugaban BUA, Abdul-Samad Rabiu ya kirkiri gidauniya ta musamman da aka sama suna ‘Gidauniyar ASR’, an kirkire ta ne domin taimaka wa jama’a.” “Bayan ya yi aiki tukuru a matsayin dan kasuwa. Abdul-samad ya fara tunanin taimakawa jama’a, inda yake son inganta rayuwar ‘yan Nijeriya da kuma ‘yan Africa.”
“A wannan gidauniyar, ana ware makudan kudade duk shekara da suka kai Dala miliyan 100 wajen taimaka wa jama’ar Nijeriya da kuma Africa.
An kasa kudin gida biyu, rabinsu an ware don tallafa wa a Nijeriya, rabin kuma an ware wa Africa.” A jawabin da ya yi lokacin amsar tallafin, mukaddashin shugaban jami’ar ya gode wa gidauniyar Abdul-Samad Rabiu (ASR) da gaba daya tawagar Kamfanin BUA bisa wannan hubbasa da suka yi. Farfesa Ekanola ya kara da cewa hukumar makarantar za ta yi amfani da wannan tallafin wajen ba da horo ga dalibanta domin su zama wadanda za’a yi alfahari da su a duniya.

What's On Your Mind?