Brazil Tana Son Neymar Ya Buga Mata Wasannin Olympic

0
88

Brazil Tana Son Neymar Ya Buga Mata Wasannin Olympic

Hukumar kula da kwallon kafar Brazil, ta mikawa kungiyar kwallon kafa ta PSG bukatar baiwa dan wasan gabanta, Neymar Junior damar buga wasa a wasannin da kasar za ta faffata ya yin gasar Olympic a Tokyo.

A wata zantawar kocin na Brazil da jaridar wasanni ta Globo, ya ce Neymar na daga cikin ‘yan wasansu sahun gaba da su ke fatan su buga wasa yayin gasar ta Olympic ganin irin bajintar da ya nuna a makamanciyar gasar cikin shekarar 2016 a birnin Rio de Janeiro.

Sai dai shi da kansa da Kocin na Brazil ya ce abu ne mai wuya PSG ta amince da bai wa dan wasan dama la’akari da yadda ya ke shirin buga wasa a gasar Copa America tsakanin ranakun 13 ga watan Yuni zuwa 11 ga watan Yuli.

“Tabbas abune mai wahala kungiyarsa ta iya lamunce masa domin ya buga mana wannan gasa amma muna bukatar hakan kuma mun rubuta musu bukatar mu sai dai muna jiran amsa daga wajensu” in ji kociyan na Brazil

Ya ci gaba da cewa “A waccan gasar shi ne ya jagoranci tawagar information samu damar lashe kofin wanda kuma mune muka karbi bakunci saboda haka a yanzu ma muna fatan zai sake samun dama domin yazo ya taimakawa matasan ‘yan wasan mu domin su samu nasarar da muke bukata”

Gasar ta Olympic dai za ta fara ne kwanaki 10 bayan Copa America kuma za a kammala ta ranar eight ga watan Agusta wato kwanaki 2 bayan bude sabuwar kakar gasar Ligue 1 a Faransa wanda ke nuna abu ne mai wuya PSG ta baiwa dan wasan dogon hutu na tsawon kwanakin.

Karkashin dokokin kungiyoyin Turai dai kowacce kungiya na da damar hana dan wasan halartar kowacce irin gasa matukar ba FIFA ce ta shirya ba kuma hakan yana nufin PSG tana da damar hana Neymar tafiya buga gasar wadda ya taimakawa Brazil din ta lashe shekaru hudu da suka gabata.

What's On Your Mind?